ZABEN KOGI: Sanata Dino Melaye da Adeyemi sun sake sa zare

0

A daidai lokacin da ake kada kuri’ar zaben gwamnan jihar Kogi, a yau Asabar, a daidai lokacin ne kuwa wasu ‘yan shiryyar Sanata na Yamma, za su zabi sanata, bayan da kotu ta bayar da umarnin cewa a sake zaben da Sanata Dino Melaye ya kayar da Smart Adeyemi.

Za a sake wannan zabe ne a kananan hukumomi bakwai, inda Adeyemi zai tsaya a APC shi kuma Dino a PDP.

Dukkan ‘yan takarar biyu dai a Karamar Hukumar Ijumu su ke.

Yayin da Adeyemi ke garin Iyara, shi kuma Melaye haifaffen Aiyetoro ne.

Adeyemi tsohon dan PDP ne da ya ci sanata daga 2011 zuwa 2015. Sai dai kuma zaben 2015, Dino Melaye na APC ya kayar da shi. Haka nan kafin zaben 2019, su biyun sun yi canjin jam’iyyu, inda Dino ya koma PDP, Adeyemi kuma ya koma APC.

Dino ya kayar da Adeyemi a har ila yau a zaben 2019. Sai dai kuma an kai Dino kara, inda kotu ta ce a sake zabe a yau Asabar.

Dino ya daukaka kara, sai dai Kuma Kotun Daukaka Kara ita ma ta jaddada cewa a sake zabe. Yanzu haka su na can su na fafatawa, ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare.

Share.

game da Author