Duk da kokarin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ke yi wajen kokarin ta gudanar da zabe sahihi, karbabbe kuma mai inganci, hakan bai hana wasu batagari da baragurbin ’yan jagalisar siyasa yin hobbasan dagula al’amurran zabe a kasar nan ba.
Idan za a bi ta karin maganar da Bahaushe ke cewa, ‘Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake ganewa’, to kuwa tun ma daga ranar Litinin za a iya yin takoke ko tababa ko shakkun wanye zabukan gwamnonin da za a gudanar gobe Asabar a jihohin Bayelsa da Kogi lami lafiya.
Irin yadda ake yawo da makamai da kuma kai wa jam’iyyun adawa hare-hare a lokutan kamfen, ya nuna cewa manyan siyasar jihohin sun shirya tsaf wajen amfani da wasu hanyoyin cin zabe. Idan ma kuri’a ba ta yi tasiri ba, to makudan kudade ko harsashe ko kafceciyar adda ko wani zandamemen takobi zai yi musu aiki.
Makonni biyu da suka gabata, an yi taron masu ruwa da tsaki tsakanin jam’iyyun da za su fafata zaben gwamna a jihar Bayelsa, tare da Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da sauran shugabannin jam’iyyu.
Irin yadda taron bai wanye lafiya ba, ya karke da yi wa shugaban INEC buyagi da hargowa, ya sa an tashi daga taron babu shiri, ballantana a rufe taron da addu’a.
Tashe-tashen hankula da suka rika faruwa kan batun takarar a jihar sun kara jefa shakku da tsoro a zukatan jama’a.
Dillancin Kuri’a Daya Kan Naira 500 a Bayelsa Da Kogi
Wani rahoto kuma da wata mashahuriyar Kungiyar Sa-ido Kan Zabe, mai suna YIAGA, ta bayyana cewa masu katin jefa kuri’a a zaben gwamnan Bayelsa da Kogi, sun maida hankali wajen sayen da ’yancin kan kudade kalilan, daga naira 500 zuwa naira 1,000.
Bangaren YIAGA mai sa-ido kan shirye-shiryen zabe, mai suna WTV ne ya fito da wannan bayan ya yi wani kwakkwaran bincike a jihohin guda biyu dukkan su.
Bincike ya kara tabbatar da cewa jam’iyyun siyasa na bi gida-gida su na daukar sunayen masu jefa kuri’a da lambar katin jefa kuri’ar su, ko dai su na ba su kudi domin zabe, ko kuma suna daukar sunayen su, da nufin biyan su naira 500 zuwa naira 1,000 idan sun zabi jam’iyyar su.
A ranar Laraba ne dai Majalisar Dattawa ta amince a bai wa Jihar Kogi zunzurutun kudi har naira bilyan 10.069, matsayin wasu kudade da ta ke bin gwamnatin tarayya bashi, na ayyukan gina wasu titinan gwamnatin tarayya da ta yi.
Wasu sanatocin sun nuna rashin amincewa da bayar da kudin ga Jihar Kogi, bisa tsoron kada a yi amfani da kudaden wajen cin zaben gwamna da za a yi da tsiya ko da tsinin-tsiya.
Yakin Neman Zabe Ko Gwajin Makamai?
Tun ana saura mako daya kafin zabe ake ta fama da rikice-rikice a wurin yakin neman zabe da kuma kai hari kai tsaye a kan wata jam’iyya daga wata jam’iyya a Jihar Kogi.
Dama ita Jihar Kogi ta yi kaurin suna shekara da shekaru wajen rikice-rikicen zabe. Kisa, sara, harbi, banka wuta gobara ta tashi, ko hargitsar rumfunan zabe da cibiyoyin kirga kuri’u, ba karamin aiki ba ne a jihar Kogi.
Na baya-bayan nan shi ne wanda aka kai wa shugabannin jam’iyyar PDP na Shiyyar Sanatan Kabba, wato Kogi ta Yamma, sun sha da kyar a ranar Larabar da ta gabata.
Wasu rikakkun ’yan takifen siyasa ne suka kai mummunan hari, abin da ya kara dagula matsalar tsaro a jihar, kwanaki biyu kafin ranar zabe.
Daga cikin wadanda aka fatattaka har da Joseph Dada, wanda aka ratattaka wa gidan sa da motocin sa ruwan harsasai ratatattata.
Sauran wadanda aka kai wa harin sun hada da Johnson Abejinrin da kuma wani mai suna Obagbayi, wanda shi ma aka ce babban dan jam’iyyar PDP ne a garin Kabba.
Hotunan da suka rika yawo a shafukan kafofin sadarwa sun nuna yadda aka ratattaka wa gine-gine da motoci harsasai. Kuma an ga yadda aka ragargaza gilasan motoci.
Rahotanni daga Jihar Kogi sun tabbatar da yadda ake ta kai wa jam’iyyun adawa munanan hare-hare.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa tuni wasu shugabannin jam’iyyun adawa sun kwashe iyalan su daga jihar zuwa wasu jihohin.
Irin yadda ake amfani da makamai a Jihar Kogi ya kara tabbatar da irin mummunar barazanar da zaben Gwamnan Jihar Kogi zai fuskanta.
Domin a ranar Talata ‘yan daba dauke da muggan makamai sun kai wa hedikwatar jam’iyyar SDP a Lokoja hari, suka banka ma ta wuta, har gobara ta lashe hedikwatar.
An kuma kekketa takardun bayanai na gudanarwar ofishin tare da ragargaza wasu kayyaki masu daraja.
Kuma a kan idon jami’an tsaro suka rika cin zarafin ‘yar takarar gwamna a karkashin SDP, Natasha Akpoti. An tabbatar da cewa magoya bayan Gwamna Yahaya Bello ne suka yi wannan aika-aika.
Abin takaici ne kwarai ganin cewa an kai wa Natasha harin ci ma ta zarafi a hedikwatar Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC na Jihar Kogi. Kuma a lokacin an je taro ne har da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Muhammad Adamu.
Duk da cewa ’yan sanda ba su karyata kai wa Natasha hari da magoya bayan Gwamna Bello suka yi ba, har yau ko mutum daya ba su kama ba.
Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar GDPN, Dele Williams ya bayyana wa PREMIUM TIMES a cikin wata tattaunawa da jaridar nan ta yi da shi cewa an sha kai wa kwanba din kamfen din sa hari a kwanakin da ya shafe ya na rangaden yakin neman zaben da ya fito takara, wanda za a gudanar ranar Asabar mai zuwa.
Ya ce wasu shugabannin jam’iyyar su ko dai sun fice daga jihar saboda tsoron rasa rayukan su, ko kuma wasun su sun fice da iyalan su daga jihar, saboda tsoron kada a kai wa iyalan na su hari.
“Baya ga cin zarafin mu a lokacin kamfen, har barazanar rasa raina sai da aka yi min.” Inji Williams.
Ya kara da cewa duk da sun kai koke-koken su ga Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan, har yau ko fara ba a kama ba. Ga shi kuma rashin tsaron sai kara muni ya ke yi a daidai lokacin da ranar zaben ke kara gabatowa.
Sai dai kuma Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Kogi, Jibrin Abu, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa bai kamata a rika ta’allaka rikicin da magoya bayan APC ba, saboda magoya bayan jam’iyyar a cewar sa, masu bin doka da oda ne.
Kisan Mutum Shida A Bayelsa Tun Kafin Ranar Zabe
Harin da aka kai wa mambobin jam’iyyar PDP a garin Ogbolomabiri-Nembe, wanda ya yi sanadiyyar kisan mutane shida, ciki har da ma’aikacin gidan talbijin wata jarida mallakar jihar, mai suna Simon ya sa dan takarar jam’iyyar PDP a zaben na gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya yi kira da a sa dokar-tabaci a yankunan da ake tashe-tashen hankulan siyasa a dalilin wannan zabe na gwamna.
Diri ya bayyana shakkun yadda za a iya barin INEC har ta gudanar da zabe a cikin adalci, sahihi, ingantacce, kuma karbabbe a wadannan yankuna da ake rikicin siyasa.
Dan takarar ya kara da cewa matsawar jami’an tsaro ba su dauki kwakkwaran mataki a yankin garuruwan Bassambiri da Ogbolomabiri da Nembe ba, to harigido kawai za a yi, ba za a bar jami’an INEC su yi zaben da ya dace ba.
Kamar wasu ‘yan siyasa a jihar Kogi, shi ma Diri ya ce wasu ‘yan siyasar yankin Nembe da ke Bayelsa, tuni sun washe iyalan su daga yankin, saboda tsoron yadda za ta kasance a lokacin zaben.