‘Yan sanda sun san za a yi tashin hankali a zabukan Bayelsa da Kogi –Sufeto Janar

0

Sufeto Janar na ’Yan Sanda Muhammad Adamu, ya bayyana cewa dama jami’an tsaro na da masaniyar za a yi tashin hankali a zabukan gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi.

Mazauna jihohin biyu sun fita sun jefa kuri’ar zaben gwamna, a ranar 16 Ga Nuwamba, amma dai rikicin da ya faru a jihar Kogi na fi na Bayelsa muni sosai.

Masu lura da sa-ido kan zabe, sun hakkake cewa jami’an ‘yan sanda sun taka rawa wajen dukkan rikicin.

Amma kuma hukumar ladafta ‘yan sanda ta musanta hannun jami’an ta a ciki. Rundunar kuma a jiya ta fito ta bayyana cewa dukkan wadanda ake cewa sun saka kayan ‘yan sanda sun yi rikici, ba ‘yan nsada ba ne, jabu ne kawai.

Hukumar ‘Yan Sanda ta dora laifin rikicin a kan karancin jami’ai masu yawa, duk kuwa da ‘yan sanda dubu talatin da biyar (35,000) da aka dankara a jihar Kogi.

Adamu ya ce jami’an tsaro sun yi nazarin jihohin da yadda yananin jama’a su ke tun kafin ranar zabe.

Ya tunatar da wasu tashe-tashen hankula da suka faru kwanaki kadan kafin zabe, inda ya ce ta nan suka tabbatar da cewa za a yi rikici sosai a ranar zabe.

“Saboda tun a lokacin kamfen mun ga yadda bangarori ke ta fada da junan su, sai muka yi wa hakan shirin sa.”

Haka ya bayyana wa manema labarai bayan ya fito daga wata ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ci gaba da cewa a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki, shi da Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa, sun je jihar Bayelsa, kuma sun je Kogi.

Adamu ya ce bayan bangarorin jam’iyyu masu yin takara sun sanya hannu kan yarjejeniyar a yi zabe ba tare da tashin hankali ba, sai sabani ya faru a zauren taron. Har ta kai ‘yan sanda sun yi amfani da barkonon-tsohuwa.

“Don haka mun san zaben ba zai gudana lami-lafiya ba, shi ya sa muka yi masa kyakkyawan shiri.”

Sai ya wanke jami’an sa ya ce wadanda aka gani su na hargitsa zabe, ba ’yan sanda ba ne, sojojin haya ne suka yi shigar-burtu sanye da kayan ‘yan sanda.

Ya ce a lokacin zaben, duk jami’an da ake gani su na gilmawa, to ya na da wani bajo a jikin kakain sa, to shigar-burtu ya yi.

An bada rahoton mutuwar mutum 10 a jihar Kogi, ciki kuwa har da dan uwan Sanata Dino Melaye.

Share.

game da Author