INEC ta bada naira milyan 1.9 ga iyalan dan NYSC da ta rasa ran ta

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayar da tallafin kudi na jinkai har naira milyan 1.9 ga iyalan wata mai bautar kasa (NYSC) da ta rasa ran ta sakamakon hatsarin mota.

An bayar da kudin ga magajin marigayiyar, da kuma wata ‘yar’uwar sa mai suna Folasade Adeyemi, a ofishin INEC da ke Ibadan.

Idan za a iya tunawa dai, Adeniran ta gamu da ajalin ta ne a kan hanyar ta daga dawowa halartar horon aikin zabe. Hatsarin ya faru cikin watan Fabrairu, 2019, a lokacin ta na aikin bautar kasa a Karamar Hukumar Ona-Ara cikin Jihar Oyo.

Kwamishinan Zabe na Jihar Kogi, ya ce INEC ta bayar da tallafin kudaden ne a bisa ka’idar da dokar hukumar ta gindaya dangane da biyan diyyar inshorar rayukan ma’aikatan ta da kuma ma’aikatan wucin-gadi na Hukumar Zabe.

“INEC na kara mika ta’aziyyar ta da kuma kara nuna jimamin rashin ta da aka yi.” Haka Kwamishinan Zabe Agboke ya fada a lokacin da ya ke mika wa dangin mai mutuwar cakin kudi na naira milyan 1.9.

“Duk da dai INEC ta na biyan kudin inshorar rayukan ma’aikatan ta da ma’aikatan wucin-gadi, wannan tallafi da ake bayarwa ba wata tsiya ba ne, idan aka yi la’akari da darajar ran da aka yi rashi.

“Wannan dai wasu ‘yan kudi ne kalilan da hukumar ta bayar domin su dan toshe wa iyalan ta wata ‘yar kafar dawainiyar jimamin rashin da aka yi.”

Agboke ya gode wa irin kokarin da masu bautar kasa suke aiwatarwa wajen ganin an yi sahihin zabe a kasar nan.

Share.

game da Author