Kotu ta tsige ‘yan majalisar dokokin jihar Kaduna biyu

0

A ranar Talata ne kotun daukaka kara dake Kaduna ta tsige wasu ‘yan majalisar dokokin jihar biyu.

Kotun ta kuma umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta sake gudanar da zabe a kananan hukumomin Kagarko da Sanga.

Alkalin kotun Daniel Kaliop ya kuma tabbatar da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yanke a tun farko.

Idan ba a manta ba a baya can ne Nuhu Shadalafiya na jam’iyyar APC ya shigar da kara a kotun sauraron kararrakin zabe kan rashin amincewa da nasarar da Morondia Tanko na jam’iyyar PDP ya yi a zaben majalisar dokoki na karamar hukumar Kagarko.

Kotun ta yanke hukunci a sake yin zabe a wasu mazabu da rumfunar zabe a Kagarko. Tanko ya shigar da kara a kotu cewa kotu ta tabbatar da shi ne yayi nasara a zaben majalisar dokoki na jihar.

Za a sake zabe a mazabu 22 da ke kagarko.

Daga nan ma kotun daukaka kara ta yanke hukunci a sake zaben dan majalisar dokoki mai wakiltan mazabar Sanga bayan kotun dake sauraron kararrakin zabe ta tabbatar da nasaran da Comfort Amwe daga jam’iyyar PDP ta yi.

Comfort itace kadai mace dake majalisar dokoki na jihar Kaduna wanda a yanzu haka Gambo Danga daga jam’iyyar APC ya shigar da kara a kotun dauka kara na rashin amincewa da hukuncin kotun saurarron kararrakin zabe ta yanke.

Share.

game da Author