Wani shirgegen bera ya hana jirgin sama tashi tsawon sa’o’i 12

0

Wani shirgegen bera ya hana jirgin zirga-zirga na cikin kasar Indiya tashi, yayin da ya rika sagarabtu a cikin jirgin, daidai lokacin da ya ke shirin cillawa sama.

Rahoto da kuma kafafen yawa labarai a yau Talata sun ruwaito cewa jirgin kirar India Flight Al-952, ya yi shirin tashi ne daga filin saukar jirage na Hyderabad zuwa garin Vishakapatnam da ke bakin ruwa a shekaranjiya Lahadi.

Jirgi ya fara lulawa kasa kafin ya cira sama, sai fasinja suka ga wani murgujejen bera na sagarabtu ya na karakaina a karkashin kafafun fasinjoji.

Dukkan fasinsojin cikin jirgin sun firgita, kuma nan da nan suka fara hargowa da kakabi. Hakan ta sa tilas jirgin ya tsaya, dukkan fasinjoji suka fita. Yayin da su kuma ma’aikata suka shiga kakarniyar neman beran.

Ba a samu nasarar zakulo shi ba sai bayan awa 10, sannan aka yi wa gaba dayan cikin jirgin feshin magani.

Bayan an dauki lokaci kuma, daidai bayan sa’o’i 12, sai aka umarci dukkan fasinjojin su yi hakuri su sake shiga. Daga baya jirgin ya lula zuwa garin na Vishakapatnam.

Jaridar Times ta Indiya da jami’an Harkokin Sufurin Jiragen Indiya duk sun tabbatar da afkuwar lamarin.

Idan za a iya tunawa, cikin 2017 ma sai da irin haka ta faru, inda aka ci karo da wani karsagin bera a cikin jirgin saman Air India, wanda ya tashi daga New Delhi zuwa San Fransisco.

Ba a dai san dalilin da ya sa ake samun beraye cikin jiragen ba. Koda ya ke wani jami’i na tunanin ta kofar da ake shigar da kayan abinci a cikin jirgi su ke fakar jami’a tsaro su shige ciki.

Share.

game da Author