Majalisar Dattawa ta nemi a hana shigo da atamfa, shadda da yaduka tsawon shekara biyar

0

A ranar Talata ne Majalisar Dattawa ta roki Gwamnatin Tarayya cewa ta dakatar da shigo da kayan atamfofi, leshi, shadda da sauran yadukan da ake shigowa da su daga kasashen waje har tsawon shekaru biyar.

Wannan bukata da kira ya biyo bayan wani kudiri ne da Sanatan Katsina ta Tsakiya, Kabir Barkiya ya gabatar, wanda ya ce, “Akwai butakar gaggawa ta farfado da masakun Najeriya da suka durkushe”.

Majalisar ta kuma roki Gwamnatin Tarayya ta samar da wadatattar wutar lantarki ga wadannan masaku domin samun damar farfadowa.

An kuma yi kira da a kara wa masu wadannan masana’antu kwarin guiwa ta hanyar ba su lamunin kudade ba tare da narka musu kudin ruwa mai tsauri ba, ta hanyar Bankin Inganta Masana’antu.

Da ya ke gabatar da kudirin, Barkiya cewa ya yi masana’antun da ake saka yaduka a Najeriya sun taka muhimmiyar rawa wajen habbaka tattalin arzikin Najeriya a shekarun 1960 har zuwa karshen 1970.

“Masaku a kasar nan sun taba kasancewa su ne ke bayar da gudummawar tattalin arziki har kashi 67 bisa 100 ya zuwa 1991. Kuma su ke da ma’aikata kashi 25 bisa 100 na dukkan masana’antun kasar nan.

“A wannan lokacin banda ma’aikatan gwamnati, babu ma’aikatan da suka fi na masaku yawa a kasar nan.”

Daga nan sai ya nuna cewa cikin shekarun nan 20 masakun Kaduna, Kano da na Aba duk sun durkushe, wanda dalilin haka dimbin jama’a suka rasa aikin yi.

Barkiya ya kara da cewa wasu tsare-tsaren da gwamnatocin baya suka rika shigo da su, kamar karin haraji, tsadar sassafa kaya ko kera su a nan cikin kasa da kuma damar da aka bayar na shigo kayan masaku irin su atamfofi shadda da sauran yaduka, sun haifar da babbar matsala da dorewar masakun Najeriya.

Daga nan sai ya kara yin nuni da cewa farfado da masakun cikin gida zai kara samar wa kasar nan kudaden shiga.

Yayin da wasu sanatoci suka goyi baya, wasu kuma ba su goyi baya ba, su na ewa matukar babu wadataccen lantarki a kasar nan, to masana’antu ko masaku ba za su iya yin wani tasiri ba.

Share.

game da Author