Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta ce tana kokarin farfado da kamfanonin sarrafa magungunan dake kasar nan domin samun daman sarrafa kashi 60 bisa 100 na magungunan da ake shigowa da su daga kasashen waje.
Shugaban hukumar Moji Adeyeye ta sanar da haka a taron manema labarai a Abuja ranar Litini.
Adeyeye ta ce farfado da kamfanonin zai taimaka wajen hana shigo da jabun magunguna wanda ya karade kasar nan yanzu.
“Wani abin tashin hankali da hukumar NAFDAC ke fama da shi shine jabun magunguna wanda ke nema ya mamaye kasuwanin kasar nan.
“ Mun gano cewa wasu daga cikin jabun magungunan da ake shigo dasu suna dauke ne da shaidar rajistar hukumar NAFDAC tun daga can ake lafta musu tambarin mu, wasu kuma tsuran su aka shigowa da su.
Adeyeye ta ce hukumar a shirye take domin bada lasisin sarrafa magunguna na tsawon shekaru biyar ga duk kamfanin sarrafa magunguna da hukumar ta amince da ingancinsa a kasar nan.
Ta ce da zarar wadannan kamfanonin sun fara aiki hukumar za ta yi amfani da magungunan da aka sarrafa su a kasar nan wajen gano jabun magungunan da ake shigo da su.
Adeyeye ta kuma ce hukumar ta inganta hanyoyin inganta magungunan da ake shigowa da su daga kasashen waje musamman wadanda ake shigo da su daga kasashen Chana da Indiya.
“Kafin a loda magungunan a jirgi zuwa kasar nan sai mun duba su tatas sannan bayan sun iso Najeriya kuma za mu sake duba su da yin gwaji a akai.
Idan ba a manta ba a watan Mayu da ya gabata ne tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar ya koka kan yadda jabun magunguna suka karade kasar nan.
Abdulsalam ya yi kira ga kungiyar NIPSS da ta ci gaba da aikin sa ido kan jabun magunguna da magungunan da wa’adin aikin su ya cika.
Ya fadi haka ne saboda sakamakon binciken NOIPOLLS, ya nuna cewa kashi 18 bisa 100 na ‘yan Najeriya na fama da jabun magunguna da kuma magungunan da lokuttan aikin su ya cika.
Sannan hukumar NAFDAC ta bayyana cewa kashi 17 bisa 100 na magungunan dake kareda kasar nan jabu ne.