A jawabin da Shehun Bama ya yi a wajen taron Maulidi da aka yi a fadarsa, mai martaba Kyari El-Kanemi ya sanar wa dandazon mutane da suka halarci wannan buki cewa daga yanzu ya ba da izinin a rufe duk wani gidan karuwai dake masarautar sa.
El-Kanemi ya ce yin haka zai rage ayyukan batagari da ‘yan iska dake tattaruwa a wannan wurare.
Mai martaba Shehu ya ce rufe irin wadannan miyagun gidaje a masarautar sa ya zama dole saboda gidaje irin haka sun fara yawa musamman a yankin Galadima.
El’Kanemi yace a dalilin haka ya umurci duk masu unguwanni da dagatai da su sa ido.
El-Kanemi ya yi kira ga iyaye da su gaggauta yi wa ‘ya’yan su allurar rigakafi domin kare su daga kamuwa da cututtukan dake kisan yara kanana.
Ya kuma yabawa namijin kokarin da dakarun sojin Najeriya, gwamnatocin tarayya da jihar Barno suka yi kan samar da zaman lafiya a jihar sannan kuma ya roki mutane da su rika yawaita addu’o’i domin Allah ya jadda zaman lafiya a jihar.
Idan ba a manta ba a watan Yulin da ya gabata ne El-Kanemi ya dawo garin Bama tun bayan hare-haren Boko Haram da ya sa dole ya fice daga garin.