• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    HANYAR DAMATURU ZUWA BIU: Yadda matafiya ke cin kwakwa Tsawon shekaru 9 an kasa kammala gyaran titin kilomita 125

    Kotu ta kwato maka-makan gidaje 48 a hannun tsohuwar Shugabar Hukumar NSITF

    KARKATAR DA NAIRA MILIYAN 289: EFCC ta gurfanar da wasu jami’an gwamnatin Katsina a kotu

    Gwamna Uba Sani ne ya yi  Ruwa ya yi Tsaki a takara ta ba mahaifina El-Rufai ba – Bello El-Rufai

    FALLASA RUFA-RUFAR HADI SIRIKA: Majalisar Tarayya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Nigeria Air

    Sanata Wamakko ya yi tir da kisan kiyashin da aka yi a tangaza, jihar Sokoto

    Atiku ya kafa gaggan lauyoyi 18, ya ce su tashi tsaye su ƙwato masa ‘nasarar zaɓen sa’ daga hannun Tinubu

    SHARI’AR ZAƁEN SHUGABAN ƘASA: Atiku ya zargi INEC ta ƙin ba shi kwafen bayanan zaɓe duk da ya biya haƙƙin Naira miliyan 6 kuɗin karɓar bayanan

    Gwamnatin Zamfara ta zargin tsohon gwamna Matawalle da sace motocin gwamnatin jihar da wasu kayan gwamnati

    Gwamnatin Kano ta rusa katafaren bene mai hawa uku da aka yi bisa filin gwamnati da Ganduje ya raba wa ƴan uwa da abokan arziki

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    TSAUTSAYI: Yadda ‘yan bindiga suka ware da Lami Awarware da Haulatu bayan halartar taron rantsar da Uba Sani a Kaduna

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

Dan damfara ya sake yin damfarar naira milyan 365 ya na tsare a kurkuku

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
November 20, 2019
in Babban Labari
0
Prison

Prison

Hukumar EFCC ta bankado wani kasurgumin dan damfara, wanda ke tsare a kurkuku, amma daga can ya sake shirya yin wata damfara har ta dala milyan 1. Dala milyan daya dai kwatankwacin naira milyan 365 kenan.

Hope Olusegun Aroke ya shirya wannan sabuwar damfara ce daga kurkuku, inda ya ke zaman wa’adin daurin shekaru 24.

Ofishin EFCC na shiyyar Lagos, sun bayyana cewa sun bankado yadda aka yi wannan damfara ta cikin intanet, tare da amfani da wasu rikakkun ‘yan damfara da ke waje.

Sanarwar da EFCC ta fitar ta bayyana cewa akwai wadanda ake bincike dangane da zargin su da aikata laifukan damfara ta hanyar intanet, wadda aka fi sani da ‘cyber crime’.

“Bincike ya nuna ya shirya harkallar damfarar naira milyan 365 a lokacin da ya ke tsare a kurkuku, yana fuskantar daurin shekaru 24.”

Wadanda ya shirya harkallar tare da su, su ma an dade ana kokarin yadda za a kama su, tun kafin wannan damfara da suka shirya.

Daga kurkukun Kirikiri EFCC ta samu wannan labari, bayan da wani ya gulmata ma ta abin da ya faru.

Babban abin da ya fi daure wa jami’an EFCC kai shi ne yadda wannan kasurgumin dan damfara ya rika harkar damfarar sa daga cikin kurkuku.

Binciken farko da EFCC ta fara yi, ta gano Hope Aroke na amfani da internet da kuma wayar GSM a cikin kurkuku, abin da doka ta hana mai zaman kurkuku ya rika amfani da su.

Abokin Barawo shi ma Barawo ne

Wani babban abin daure kai da al’ajabi kuma shi ne yadda Hope Aroke ya samu daurin gindin ’yan sanda, har ta kai ga an kwantar da shi Asibitin Musamman na Jami’an ’Yan Sanda da ke Falomo, Lagos.

Daga asibitin kuma saboda samun daurin gindin jami’an tsaro, sai Aroke ya rika fita ya na kama otal, inda matar sa da ’ya’yan sa kan je su gana da shi.

Har ma sai da ta kai ya rika zuwa ya na gudanar da wasu uziri da sha’anin gaban sa. Haka dai binciken da EFCC ta gudanar ya tabbatar.

A yanzu kuma EFCC na ci gaba da binciken ko su wa da su wa ne ke da hannu wajen rika daukar sa ana kwantar da shi asibitin jam’an ‘yan sanda, har ya na kama hotel, ya fice kuma ya shiga gari halartar wasu lamurran gaban sa.

Daurin Gindin Jami’an Tsaro

Saboda tsananin daurin gindi, bincike ya nuna Aroke ya na amfani da sunan gare, wai shi Akinwunmi Sorinmade, har ya bude asusun ajiya a First Bank da Guaranty Trust Bank.

Daga kurkuku kuma ya sayi gida a cikin rukunin gidaje na Fountain Spring Estate, Lekki, Lagos, a cikin 2918 a kan kudi naira miliyan 22.

Sannan kuma ya sayi Lexus, motar alfarma samfurin RX 350 2018, wadda ya sai wa matar sa, Maria Jennifer Aroke.

Sannan kuma a cikin kurkukun ya na amfani da lambobin sirri na asusun cirar kudi na matar sa, wanda ya ke tura kudade kai-tsaye daga cikin kurkuku, ta hanyar amfani da wayar sa.

Ci gaba da binciken da ake yi kuma ya kara tabbatar da cewa a lokacin da ake cikin shari’a a 2015, Aroke ya sayi wani babban gida mai lamba ‘Plot 12, Deji Fadoju, Street, Rukunin Gidaje na Megamounds, a Lekki, Lagos, a kan kudi naira milyan 48.

Aroke dai daya ne daga wasu daliban Najeriya biyu mazauna kasar Malaysia da EFCC ta damke bisa laifukan damfara ta intanet a cikin 2012.

An kama su ne a wani gida mai lamba 1004, a Tsibirin Victoria Island, Lagos.

Dan asalin garin Okene ne ta jihar Kogi, wanda ya tafi birnin Kuala Lumpur da karyar wai ya na karatun Kimiyyar Kwamfuta.

Sai dai kuma EFCC ta fallasa shi cewa babban gogarman wasu ’yan damfara ne ta intanet, wanda suka shahara da damfara a nahiyoyi biyu na duniyar nan.

Bayan an kama shi, an dade ana shari’a, daga nan dai Mai Shari’a Lateefa Okunno ta Babbar Kotun Jihar Lagos ta same shi da laifuka biyu, kuma nan take ta daure shi shekara 12 a kowane laifi daya.

Ya zama shekaru 24 kenan aka daure shi.

Tags: AbujadokokiEFCCHausakwamfutaLabaraiLateefa OkunnoMilyanNajeriyaNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

Buhari ya sa hannu a dokar iko don hana yin bahaya a waje a Najeriya

Next Post

Mahara sun sace DPOn ‘Yan sanda

Ashafa Murnai

Ashafa Murnai

Next Post
gunmen

Mahara sun sace DPOn 'Yan sanda

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • HAJJI 2023: Hukumar Alhazai ta gindiya sabbin sharuɗɗan adadin kwanakin ziyara Madina
  • HANYAR DAMATURU ZUWA BIU: Yadda matafiya ke cin kwakwa Tsawon shekaru 9 an kasa kammala gyaran titin kilomita 125
  • KARKATAR DA NAIRA MILIYAN 289: EFCC ta gurfanar da wasu jami’an gwamnatin Katsina a kotu
  • DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad
  • SHARI’AR ZABEN SHUGABAN ƘASA: Kotu ta karɓi sakamakon zaɓen jihohi 17 daga hannun Peter Obi domin tantance sahihancin su

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.