Mahara sun sace DPOn ‘Yan sanda

0

Mahara dauke da muggan makamai sun sace wani shugaban ‘yan sanda na karamar hukumar mubi a hanyar sa ta dawowa daga Yola.

Kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa Suleiman Nguroje ya bayyana wa manema labarai a garin Yola, ya ce maharan sun bude wa motar da DPOn yake ciki ne inda nan take ya tsaya sannan suka arce da shi.

Sai dai kuma mazauna garin Mararraban Mubi, inda aka sace wannan dan sanda sun shaida wa manema labarai cewa an arce da DPO Ahijo Mujeli, da misalin karfe 6:30 na yammacin Talata.

Kakakin rundunar ‘yan sanda Nguroje ya bayyana cewa tuni har jami’an su sun fantsama dazukan dake kewaye da garin Mararraba diomin ceto wannan dan sanda.

Sai dai shi ya ce da misalin karfe 6:30 na yammacin Talata ne ba 8 ba.

Jihar Adamawa dai ta yi kaiurin suna wajen hare-haren ‘yan bindiga da Boko Haram. An rasa rayka da dukiyoyi da dama a dalilin wadannan hare-haren a fadin jihar.

Share.

game da Author