Buhari ya sa hannu a dokar iko don hana yin bahaya a waje a Najeriya

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a dokar iko domin kawo karshen yin bahaya a waje a kasar nan.

Bisa ga doka da shugaban Kasa ya rattaba hannu a kai, za a yi kokarin ganin an kau da wannan abu na yin ba haya a waje nan da shekarar 2023.

Shugaban kasa Buhari yayi haka ne saboda a rage yaduwar cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin bahaya a waje.

Sakamakon bincike ya nuna cewa bahaya a waje ya yi wa kasar nan katutu domin mutane miliyan 46 ne ke yin bahaya a waje.

Binciken ya kuma kara nuna cewa a cikin kananan hukumomi 774 da ake da su a kasar nan 11 kawai suka iya kawo karshen yin bahaya a waje a garuruwansu.

Ga Abin Da Dokar Take

1. Najeriya za ta zage damtse wajen ganin ta kawao karshen yin ba haya nan da 2025.

2. Ma’aikatu za su hada hannu da ma’aikatar ruwa domin ganin an zantar da matakan hana yin bahaya a waje.

3. Dokar ta bai wa ma’aikatar ruwa damar bude wani sashe na musamman domin tsaftace kasa da kuma damar gina dakunan bahaya a ofisoshi, makarantu, wuraren ibada, kasuwani, tashoshi da sauran su.

4. Ma’aikatu da hukumomin gwamnati dole su rika mara wa wannan shiri na tsaftace kasa da aka kirkiro.

5. Majalisar dokoki ta kasa da na jihohi za su yi dokar hana bahaya a waje da irin hukunci da za ayi wa duk wanda aka kama yana yin haka.

6. Dole duk wasu ayyuka na ci gaba da za a rika yi, sai an tabbatar da an samar da wuraren bahaya.

7. Za a dakatar da ayyukan wannan ma’aikata ta ‘Tsaftace Najeriya’ dsa zaran an kawo karshen yin bahaya a kasar nan.

8. Dole ma’aikatun gwamnati su bi wannan doka har sai an kai ga ci.

A watan Yuli ne sakamakon binciken da kungiyar ‘Water Aid’ ta gudanar ya nuna cewa mutane miliyan 116 ne ke kantara bahaya a waje a Najeriya.

Jami’ar kungiyar Evelyn Mere ta koka da cewa matsalar yin bahaya a waje ya karaɗe ko ina da ya haɗa da makarantu har da asibitoci.

“ Kashi 50 bisa 100 na makarantu da asibitoci a kasar nan basu da ingantattun dakunan bahaya sannan kashi 88 bisa 100 na makarantu da asibitoci basu da tsaftattacen ruwa.

Mere ta ce domin kawo ƙarshen wannan matsala ne ƙungiyar shirya shiri mai taken ‘VOTE4WASH’ wanda suka fara a lokacin zabe.

Shirin ya yi ƙoƙarin jawo hankalin ‘yan takara da ‘yan siyasa wajen daukan alkawarin kawo karshen matsalar dake tattare da yin bahaya a waje.

Share.

game da Author