Yadda Shugaban Hukumar Kula da Hada-hadar Fetur ya bijire wa umarnin Buhari

0

Hukumar Kula da Hada-hadar Cinikayyar Fetur (PEF) ta daukin nauyin wasu lauyoyi hudu zuwa taron Lauyoyi na Kasa da Kasa da Seoul, babban birnin Koriya ta Kudu.

Wannan daukar nauyin tafiye-tafiye kuwa kakara karya doka, umarni da kuma gargadi ne da gwamnatin tarayya ta yi cewa ta soke tafiye-tafiye barkatai, musamman irin wannan tafiya taro.

Ganin yadda ake gaganiyar matsalar kudaden shiga aljihun gwamnatin tarayya, sai ta soke duk wasu tafiye-tafiyen gayyar-na-gayyaro da gayyar-na-Ayye da ma’aikatan gwamnati ke fita su na halarta, tun a cikin 2015.

Gwamnati ta ce sai wata tafiya ko fita mai dalili ko matukar muhimmanci ce kadai za a iya amincewa a fita waje a halarta. Ita ma din, an bada gargadin cewa sai an nemi amincewa daga Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.

Cikin 2016 ne gwamnatin Buhari ta sake jaddada wannan mataki da gargadin hana ma’aikata fita waje taro, wanda tun a daidai karshen mulkin Jonathan cikin 2015 ne aka fito da umarnin.

Kunnen-Uwar-‘Shegun’ PEP

Maimakon a bi wannan umarni da ka’ida, Hukumar PEF ta yi kunnen-uwar-shegu da wannan gargadi, inda ta tura lauyoyi hudu kasar Koriya ta Kudu, suka halarci taro, ba tare da neman izni daga Ofishin Shugaban Ma’aiktan Gwamnatin Tarayya ba.

Binciken da PREMIUM TIMES ta gudanar ta gano cewa daga cikin lauyoyin hudu, guda uku daga Ma’aikatar Shari’a aka dauki nauyin su.

Wasu takardu da suka fado hannun wakilin mu sun tabbatar da cewa Shugaban Hukumar PEF, Ahmed Bobboi ne ya sa hannun amincewa PEF ta dauki nauyin

Halartar lauyoyin taron, wanda aka gudanar a ranakun 22 zuwa 27 Ga Satumba, 2019.

Biyu daga cikin lauyoyin ma’aikata ne a Ma’aikatar Shari’a, biyu kuma na Ma’aikatar Man Fetur da PEF ne.

Wata majiya ta shaida wa wakilin mu a asirce cewa an kashe akalla naira miliyan 11 wajen daukar nauyin lauyoyin fita waje domin halartar taron.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta kasa samun takamaimen adadin kudaden da aka kashe wajen yin wannan tafiye-tafiye.

Irin yadda aka yi gaggawar rubuta takardar neman tafiyar da kuma yadda Bobboi ya yi saurin sa mata hannun amincewa a ranar da aka rubuta takardar, shi ma abin tambaya ne.

Wadanda aka dauki nauyin tafiyar ta su zuwa Koriya ta Kudu din sun hada da Abimbola Ajileye, A’ishatu Kaltungo da Rafia Abubakar, dukkan su manyan jami’an lauyoyi ne.

An rubuta cewa za su je ne domin su halarci taro a kan harkokin fetur da gas, musamman fetur da gas na Afrika.

PREMIUM TIMES ta gano cewa a cikin rana daya aka yi komai da komai, wato daga rubuta takardar, amincewar.

Share.

game da Author