Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa an hada da sunan INEC an kai kararrakin zabe har sau sama da 1600 a sanadiyyar zaben 2019.
Yakubu ya ce wadannan kararraki duk sun bijiro ne bayan zaben 2019 da aka gudanar cikin watan Fabrairu da kuma Maris.
Ya yi wannan bayani a yau Alhamis, lokacin da ya bayyana a taron farko da shugaban na INEC ya yi da Kwamitin Majalisar Dattawa na INEC.
Farfesa Yakubu ya yi wa kwamitin bayanai daban-daban a lokacin da ya ke ba su rahoton hukumar sa tun bayan kammala zaben 2019.
Da aka tambaye shi ta ina INEC ke dibar kudin daukar nauyin sha’anin kararrakin da aka maka ta, sai Yakubu ya ce akasari sun a amfani ne da lauyoyin su da ke karkashin hukumar, wadanda yawan su bai kai yawan wadanda ake bukata domin kula da shari’un da ke gaban INEC din ba.
“Misali, bayan an kammala zaben fitar-da-gwani kafin zaben 2019, an maka INEC kara a kotuna daban-daban, sama da sau 800.
“Akwai kararraki 809 a gaban mu da suka bijiro kafin zabe, sannan kuma akwai wasu 807 da suka bijiro bayan zaben 2019. Kai ko jiya ma an maka INEC kara kotu sau uku, sakamakon abin da ya biyo bayan zaben fidda-gwani a jihohin Bayelsa da Kogi.” Inji Yakubu.
Daga nan kuma ya sanar da sanatocin irin shirin da INEC ta yi domin tunkarar zabukan gwamna a Bayelsa da Kogi da za a gudanar rana daya, cikin watan Nuwamba.
Sannan kuma Farfesa Yakubu ya yi watsi da ikirarin da wasu ke yi cewa INEC na fama da matsalar kudaden shirya zaben gwamna a Bayelsa da Kogi.
Ya ce ai akwai kudaden kasafin kudi na INEC din daban, wadanda daban su ke da kasafin kudaden zabe.
A yanzu dai akwai kararraki sama da 1600 da da suka danganci zaben 2019, kuma kowace kara sai an hada da INEC an maka kotu.
Kusan an kammala shari’un zaben gwamna, wanda har yau babu wani gwamna da kotun Daukaka Kararrakin Zaben Gwamna ta tsige.
Yayin da PDP da kuma dan takarar ta Atiku Abubakar suka garzaya Kotun Koli, domin nuna rashin gamsuwa da hukuncin da Kotun Daukaka Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta yanke.
Kotun dai ta yanke hukucin cewa Atiku da PDP sun kasa gabatar da kwararan shaidun zarge-zargen da suka yi wa zaben 2019, ballanatana har kotu ta soke nasarar da APC da dan takarar ta suka samu, a bai wa Atiku da PDP.
Discussion about this post