Buhari ya dakatar da daukar ma’aikata

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada sanarwar dakatar da dukkan hukumomin gwamnatin tarayya daga daukar ma’aikata, ba tare da neman izni dauka daga gwamnati ba.

Buhari ya yi wannan bayani a ranar Talata da ta gabata, lokacin da ya ke jawabin kasafin kudi na 2020 a Majalisar Tarayya.

Ya ce babu hukumar da za ta sake saukar ma’aikata, sai ta nemi izni kuma an bayar tukunna.

Daga nan sai ya yi gargadin cewa duk hukumar da ta karya wannan umarni, to hukunci ne zai biyo baya.

Sannan kuma ya yi gargadin cewa daga 31 Ga Oktoba, kada a kuskura a kara biyan ma’aikata albashi ba bisa tsarin tantance ma’aikata na IPPI ba.

Buhari ya ce duk jami’i ko ma’aikatar da ta kuskura ta karya wannan umarni, to zai yaba wa aya zaki.

Ya yi wannan gargadin ne yayin da ya ke jawabin bayyana kasafin kudi na 2020 a zauren Majalisar Tarayya.

Ya ce gwamnati ta fito da tsarin tantance adadin ma’aikata na IPPI domin ta rika ririta kudade tare da sa-ido kan kudaden da ake kashewa.

Baya ga wannan kuma, Buhari ya sake yin gargadi cewa an rufe kofar daukar ma’aikata a hukumomin gwamnatin tarayya ba tare da an nemi izni ba
Ya ce za a hukunta duk wanda ya kuskura ya dauki ma’aikata aiki ba tare da ya nemi izni, an amince ya dauka ba.

Ya ce ma’aikatun gwamnati za su kashe naira biliyan 400 wajen gudanar da ayyukan yau da kullum. Ciki kuwa har da sabbin ma’aikatun da gwamnatin tarayya ta kirkiro.

Sai kuma ya yi kira ga dukkan ma’aikatun su rika taka-tsantsan wajen kashe kudaden su.

Marhabin da Harajin ‘VAT’ – IMF

A wata sabuwa kuma, Babban Bankin Bayar da Lamuni na Duniya, IMF, ya yaba wa gwamnatin tarayya dangane da karin harajin jiki-magayi na ‘VAT’ da ta yi, daga kashi 5% zuwa kashi 7.5%.

IMF ta fitar da wata takarda Jim kadan bayan tashi daga wani taro, inda ta goyi bayan Najeriya kan kadin harajin na kashi 50% da ta yi.

Bankin ya ce duk da dai tattalin arzikin Najeriya ya na fama da mawuyacin kalubale, wannan karin haraji da aka bijiro da shi ya zo a daidai lokacin da zai yi tasiri.

Share.

game da Author