KASAFIN 2020: Ma’aikatu da Hukumomin gwamnati sun tsula wa kwangiloli tsada –Sanata Lawan

0

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, ya yi kira da fito da tsarin matse yawan kudaden da ake sakar wa ma’aikatun gwamnatin tarayya.

Ya ce hakan ya biyo bayan ganowar da aka yi cewa ma’aikatun na yi wa kwangiloli azuraren makudan kudade.

Lawan ya ce wannan karma-karmar tsula wa ayyukan kwangila na zuke kudaden shigar da gwamnati ke samu da nufin yin amfani da su wajen gudanar da ayyukan raya kasa.

Lawan ya yi wannan jawabi a lokacin zaman sauraren da kwamitin kasafin kudin 2020 ke yi a ranar Laraba.

“Maganar gaskiya ana tsula wa kwangiloli kudade a Najeriya. Abin da za a iya saye dala 10,000 a kwangilar wata kasa, a Najeriya sai a rubuta cewa an sayo shi a kan dala 100,000. Kuma ma’aikatun nan sun sani sarai cewa mu na fama da karancin kudaden shiga a kasar nan.

“Ina ganin fa lokaci ya yi da za mu yi wani abu a kan wannan babban al’amari. Idan har Hukumomin Gwamnatin Tarayya 10 na bukatar sayen wani abu iri daya, kuma a kasuwa daya za su sayi abin nan, don me za a samu bambancin farashi a tsakanin dukkan su 10 din? Don me? Na ce don me za a samu bambancin fasashi?

“Don haka a wannan kasafin kudin kwamtin mu zai duba wannan batun sosai idan ma’aikatu 10 kowace za ta sayi kwamfutoci, to dole ku tabbatar cewa dukkan farashin da kowace ma’aikata a rubuta za ta sayi kwamfutar ya yi daidai da na kowace ma’aikata.”

Misalin irin wannan tsawwala farashin kaya a ma’aikatu ke yi da kuma hukumomi, akwai farashin da Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC) ta rubuta za ta sayi babban janareta domin amfani da shi a ofishin ta na Lagos, a kan kudi naira milyan 26,930,992.

Amma kuma hakikanin farashin sa a kasuwar ‘online’ ta Jumia, naira milyan 19 kadai.

Share.

game da Author