Dalilin da ya sa Buhari ya canja sunan Ma’aikatar Pantami

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya canja wa Ma’aikatar Sadarwa suna, zuwa Ma’aikatar Sadarwa da Bunkasa Tattalin Arziki kasa da Fasahar Zamani.

An canja sunan ma’aikatar ce wadda Isa Fantami ne Minista a Ma’aikatar.

Fantami, wanda kafin nada shi Minista shi ne shugaban Hukumar Inganta Fasahar Zamani, fitaccen malami ne da ya yi fice a Arewacin kasar nan, kafin nada shi minista.

Ya na daga cikin ministoci mafi kankantar shekaru da Buhari ya nada a zangon san a biyu.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai ta Ma’aikatar Yada Labarai da Arzkin Fasahar Zamani ta fitar, Philomina Oshodin ta ce Buhari ya canja wa ma’aikatar suna ne bayan da Minista Fantami ya ba shi shawarar yin haka din.

Ta ce “an canja wa Ma’aikatar suna ne domin ta samu damar kara fadada ayyukan ta da kuma muradin ta na cimma kudirin inganta tattalin arzikin Najeriya ta hanyar amfani da fasahar zamani, wato EGRP, kamar yadda ya ke a cikin ajandar wannan gwamnatin.”

Sanarwar ta kara da cewa “tsohon sunan ma’aikatar ya na tafiya ne da tunani irin na da can, ba irin sabon ci gaban zamani ta amfani da fasahar ICT da shi duniya ke tafiya a kai ba.

“Kuma dama wannan sabon tsari na zamani ne Kungiyar Sadarwa ta Kasa-da-kasa (ITU) ta yarda kowace kasa ta tafi a kan sa.”

Sanarwar ta kuma bada misalai da irin yadda wasu kasashe ke amfani da fasahar zamani wajen inganta tattalin arzikin su.

Kasashen da aka buga misali da su, sun hada da Scotland, Thailand, Tunisia, Jamhuriyar Benin, Burkina Faso da sauran su.

Ta ce su wadannan kasashen har ma kirkiro Ma’aikatar Fasahar Zamani suka yi sukutun wadda ke a sahun gaban inganta tattalin arzikin su.

Tuni dai Majalisar Zartaswa a zaman ta na jiya Laraba ta amince da sabon sunan da aka rada wa ma’aikatar.

FANTAMI YA DANKA WA NCC BULALAR DUKAN KAMFANONIN WAYAR GSM

A wani labarin kuma, Ministan Sadarwa da Inganta Arzikin Fasahar Sadarwa, Isa Fantami, ya bada umarni ga Hukumar Kula da Sadarwa ta Kasa (NCC), cewa ta gaggauta bincikowa tare da hukunta duk wani kamfanin wayar GSM wanda ya fara cajin kwastomomi kudaden-alakakai, da suka kira tsarin USSD.

Sanarwar ta fito ne da sa hannun Kakakin Yada Labaran Minista, mai suna Uwa Suleiman, tare da cewa an fara cajin kudaden ta haramtacciyar hanya.

An zargi wasu kamfanonin wayar GSM da fara zukar cajin kudade ga duk wani da ya yi hada-hadar kudin banki ta hanyar amfani da wayar tarho din sa ta hannu.

An zargi kamfanin MTN da fara yin wannan haramtaccen cajin kudaden alakakai, ba tare da neman umarni daga NCC ba.

A kan haka ne aka umarci NCC ta hana kowane kamfanin wayar tarho ci gaba da zukar wadannan kudade, kuma a hukunta wanda ya rigaya ya fara.

Wannan kakkausan umarni ya biyo bayan korafe-kofare da suka karafe shafukan twitter, jim kadan bayan da MTN ya fara zuke wa kwastomin sa kudade a karkashin tsarin da suke kira USSD.

Ma’aikatar ta jaddada cewa ba za ta amince da irin wannan hawan-kawara da ake yi wa kwastomomin wayar GSM a kasar nan ba.

Share.

game da Author