Wata kungiyar sa-ido kan yadda gwamnati ke kashe kudaden ta, BudgIT, ta bayyana binciken cewa jihohi uku ne kadai ke iya tsayuwa da kafafun su a Najeriya.
BudgIT ta ce sauran jihohin kakaf duk da kudaden kasafi daga gwamnatin tarayya su ka dogara.
Rahoton da ta fitar baya-bayan nan a jiya Laraba, mai suna “ Matsayin Jihohi a 2019”, kungiyar ta ce jihar Lagos ce kadai sai kuma mai bi ma ta jihar Rivers da kuma Akwa Ibom ke iya dogaro da kan su.
Kungiyar ta ce jihohi irin Delta su na kashe makudan kudade wajen tafiyar da jihar, har naira biliyan 200.
Jihohi irin su Bayelsa duk da kankantar ta da rashin yawan al’ummar ta, ta kashe har naira bilyan 137, sai na sahun baya irin su, Sokoto, Jigawa, Yobe da sauran su.
Jihohin Kudu-maso-kudu sun fi saurann jihohi kashe makudan kudade, saboda dimbin kudaden da suke samu daga kashi 13 bisa na rarar ribar danyen man fetur da Gwamnatin Tarayya ke ba su.”
Irin haka ne inji BudgIT ta ce ya sa ake ganin jiha kamar Cross River da wani kamfacecen kasafin kudi har naira tiriliyan 1.04.
BudgIT ta gano cewa Kogi ce a sahun baya wajen fama da rashin kudi da kuma dogaro da gwamnatin tarayya, saboda gibin biyan ma’aikata albashi da jihar ta shiga a cikin 2017.
Sannan kuma ita jihar Kogi akwai matsalar biyan basussuka da ya yi wa gwamnatin jihar katutu.
“Mun yi amanna cewa idan ana so a fuskanci wani abu, to tilas sai jihohi sun fito da hanyoyin samun kudade, yadda za su iya tafiyar da kan su. Hakan cewar BudgIT, zai sa a rika samun isassun kudaden da za a inganta fannin lafiya, ilmi da kuma samun sauran damammaki.” Inji rahoton.
Shugaban binciken BudgIT, Orji Uche, ta ce jihohi 19 ne kadai ke iya wasun kudaden kashewa har ya ishe su, idan suka hada da kudaden shigar da suke samu a cikin jihar na haraji da kuma kason karshen wata da su ke samu daga gwamnatin tarayya.
Daga nan sai Uche ta yi gargadin cewa bai kamata a wannan mawuyacin halin matsalar tattalin arziki da ake fuskanta ba, kuma a ce jihohi sun kasa tashi tsaye su kara samar wa kan su kudaden shiga.
Ta ce a yanzu tunda farashin danyen man fetur ba shi da tabbas, kamata ya yi jihohi su bijiro da wasu hanyoyin samun kadade na su. Maimakon zaman dirshan din jihar kudade daga Gwamnatin Tarayya.