‘Yan soshiyal midiya ke ruruta wutar kashe-kashe a duniya – Buhari a UN

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ‘yan sohiyal midiya ne ke kara ruruta wutar rikice-rikice da kashe-kashe a cikin al’umma.

Buhari ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya ke jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, na 74, a birnin New York na Amurka.

Buhari wanda shi ne na biyar a jerin wadanda suka fara yin jawabi a ranar farko na bude taron, wato ranar Talata, ya yi kira da masu kamfanonin fasahohin zamani da su kara tashi tsaye wajen ganin sun dakile masu ruruta wutar fitintinu a soshiyal midiya.

“Ba zai yiwu a kyale wasu na ta ruruta birkitattun sakonnin haddasa rikicin addini, wariya, kin jinin bakake da labaran karya masu haddasa rikici tsakanin al’umma ba. Illar su na haifar da rasa rayukan jama’a da dama. Irin wannan kuwa kan iya haddasa wasu kasashe su tarwatse.”

Buhari ya ci gaba da cewa gwamnatin sa na fuskantar kalubalen yaki da rashawa.

Daga nan sai ya yi gargadi ga gungun ‘yan harkallar kasa-da-kasa cewa yadda Najeriya ke gurfanar da masu harkallar kwangilar P&ID, “alama ce mai nuna cewa ba za a bar wasu masu taya bera bari su zambaci Najeriya makudan bilyoyin daloli ba.”

Da ya ke magana a kan makasudin taken makalar taron, wato batun kawar da fatara da yunwa a duniya, Buhari ya ce babu babbar barazana kamar fatara da yunwa. “Daga wadannan sabubba ne ake samun fantsamar masu aikata laifuka a doron kasa, ‘yan bindiga, masu safarar jama’a da kuma fama da illolin da wadannan aika-aika ke haifarwa cikin jama’a.”

Buhari ya kara jaddada goyon bayan Najeriya don ganin an kawar da yunwa, fatara da aikata manyan laifuka da kuma wanzar da zaman lafiya a Afrika da duniya baki daya.

Share.

game da Author