Sakamakon binciken da Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da Asusun kula da al’amuran yara kanana na majalisar dinkin duniya ya nuna cewa kasashen dake Nahiyar Afrika sun yi nasarar rage yawan mace macen yara kanana da mata matuka.
Sakamakon binciken ya nuna cewa a shekarar 2000 adadin yawan yara kanana musamman ‘yan kasa da shekara biyar dake mutuwa ya ragu zuwa rabi.
Bincike ya nuna cewa yara miliyan 6.2 masu shekaru 15 zuwa kasa ne suka rasu a 2018 wanda daga ciki yara masu shekaru kasa da biyar ne da suka kai miliyan 5.3 ne suka rasu.
Sannan kuma mata sama da 290,000 sun rasu a wajen haihuwa a 2017.
Idan ba a manta ba a watan Yulin da ya gabata ne UNICEF ta bayyana cewa rashin kwararrun ma’aikata, rashin samar da ingantattun kayan aiki a asibitoci musamman a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na daga cikin matsalolin dake hana Nahiyar Afrika iya kawo karshen yawan mace-macen yara kananan da mata a kasashen su.
A binciken da asusun ta gudanar a 1999 zuwa 2015 ya nuna cewa an samu raguwar kashi 43 daga cikin 100 na yawan mace-macen yara kanana da mata.
Sai dai kuma duk da haka binciken ya nuna cewa kasashen dake Nahiyar Afrika na da sauran aikin da ya kamata ta yi domin samun nasaran kawar da yawan mace macen yara kanana da mata kuma.