Buhari ya yi tir da yunkurin juyin mulki a Ghana

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tir da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a kasar Ghana. Ya ce zabe ta hanyar dimokradiyya ce hanya kadai karbabbiya wajen kafa gwamnati a Afrika.

Gwamnatin kasar Ghana ta ce an yi yunkurin juyin mulkin, ana saura kasa da shekara daya a gudanar da zabe a Ghana.

An ruwaito cewa jami’an tsaro ne suka tarwatsa aniyar masu kokarin juyin mulkin, watanni 15 ana sa-ido a kan masu kitsa tuggun da ake zargi.

Daga baya gwamnatin kasar Ghana ta bayyana sanarwar kama wasu uku da ake zargi da hannun su dumu-dumu a yunkurin juyin mulkin.

An bayyana su da cewa mambobi ne na wata kungiya mai suna ‘Take Action Ghana.’

Ministan Yada Labarai na Ghana, Kojo Nkumah, ya bayyana cewa kungiyar na bai wa matasa horo domin tarwatsa kasar Ghana.

Yayin da Buhari ke magana a yau Laraba ta bakin kakakin yada labaran sa, Garba Shehu, ya bayyana cewa Najeriya da Ghana aminan juna ne a karkashin kungiyar Hada kan Kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS da kuma ‘Transparency International’ da sauran su.

“Hanya daya abar amincewa wajen kafa gwamnatin dimokradiyya ita ce hanyar gudanar da zabe. Lokacin da ake kafa gwamnati ta hanyar juyin mulki ba tare da kuri’u ba a Afrika ya wuce, ya zama tarihi.

“Ina kira duk kasashen Afrika su rike Ghana da mutunci, kamar yadda mu Najeriya mu ka rika ta a matsayin kasa mai martaba kuma abokiyar tafiyar ‘yan uwantaka tsakanin juna.” Inji Buhari.

Share.

game da Author