Alamomin tabarbarewar wutar lantarki sun kunno kai a kasarv nan, yayin da kamfanonin saida wuta, wato GENCOs suka yi wa gwamnatin tarayya barazanar janyewa daga saye da sayar da wuta.
Hakan ya biyo bayan wasu makudan kudade har naira bilyan 2.7 da aka nemi kowanen su ya biya.
An ce kudaden da ake so su biya din cajin kudaden gas ne da kuma cajin NBET.
NBET kamfani ne da Gwamnatin Tarayya ta kafa mai shiga tsakanin harkar kudade tsakanin gwamnati da kamfanonin saida wutar lantarki ta hanyar goyon bayan harkar zuba jari ta NESI.
Matsalar da ta shiga tsakani ce ta sa har gwamnatin tarayya nemi zuba naira biliyan 600 domin tallafa wa GENCOs su samu sa’idar harkar lantarki a fadin kasar nan.
Sai dai kuma GENCOs sun bayyana cewa ba za su amince da wannan caji na naira bilyan 2.7 da aka kakaba musu da rana tsaka ba.
Babban Sakatariyar Kungiyar Kamfanonin Raba Wutar Lantarki, GENCOs, Joy Ogaji, ta ce NBET tun a ranar 13 Ga Satumba ya bada umarnin biyan kudaden ko kuma su fuskanci matsalar rashin wadatar da su da gas.
Kitimirmira
Ogaji ta ci gaba da nuna takaicin yadda NBET ya sanar da su cewa kamfanin na NBET wai ya samu amincewa daga Fadar Shugaban Kasa ya ci gaba da bin ba’asin kudaden gas daga kamfanonin GENCOs, ta hanyar dora musu cajin da tilas sai sun biya, kafin a kai ba su kudaden ceto su daga durkushewa har naira bilyan 600.
Daga nan ta ce wannan caji da aka dora musu ya yi tsauri sosai, kuma haramtacce ne. Daga nan ta ce babu wata hujja gamsassshiya da aka nuna musu cewa su karbi kudaden daga hannun kamfanonin sayar da wutar lantarki.
“Mu dai ba mu san da wadannan kudaden ba. Haramtattu ne, kuma tsawwalawa ce kawai.”