Hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Tarayyar Turai (ROLAC) ta bude wani fanni a babbar asibitin Enugwu-Ukwu dake karamar hukumar Njikoka a jihar Anambara domin duba wadanda aka yi wa fyade a jihar.
Darektan cibiyar Bernadette Uchendu ta sanar da haka wa manema labarai a garin Enugwu-Ukwu a makon da ya gabata.
Uchendu ta ce asibitin za ta rika duba wadanda aka yi wa fyade a jihar kyauta.
“Abin da muke bukata daga wurin su shine hujojin da za su tabbatar cewa lalle an yi wa mutum fyade wanda lauyoyi da jami’an tsaro za su yi amfani da shi wajen kwato musu ‘yanci.
“A dalilin haka muke kira ga duk mutanen da aka yi wa fyade da su hanzarta zuwa asibiti domin a duba su.
Ta ce asibitin na da kwararrun ma’aikata da ingantattun kayan aiki sannan ta yi kira ga mutane da su rika tona asirin masu aikata wannan mummunar abu.
Idan ba a manta ba a cikin watan Satumban nan ne jami’an tsaro a jihar Akwa Ibom suka kama wani tsoho mai shekara 70 da laifin yi wa ‘yar shekara bakwai fyade.