• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    ZAƁEN KANO: Ganduje, Gawuna Garo da APC sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓe, sun yi zanga-zanga a Kano

    Ba ayi zabe a Katsina ba, coge aka yi kuma za mu garzaya Kotu – Lado-Danmarke

    Hyacinth Alia na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Benuwai

    Umar Bago na APC ya lashe zaben gwamnan Neja

    KURUNKUS: Abba Gida-Gida ya doke ɗan takaran Uban Abba, Gawuna na APC da kuri’u sama da miliyan ɗaya a Zaɓen gwamnan Kano

    ZAƁEN GWAMNAN JIGAWA: Namadin APC ya natsar da Lamidon PDP a Jigawa, ya lallasa shi da kuri’u 618,449

    Thugs-attack-collation

    ZAƁEN GWAMNONI YA ƊAU ZAFI: An kashe shugaban PDP bayan an lakaɗa masa dukan tsiya a rumfar zaɓen sa

    2023: Ya mutan Adamawa, ga Tinubu ga Binani na kawo muku su – Shelar Buhari a Yola

    ADAMAWA TA KWASHI ‘YAN KALLO: Binani ta kamo hanyar tururmusa ƙarti 14 a kokawar ƙwace kujerar gwamna

    ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: Muhimman Abubuwan Da Suka Faru Daga Ƙarfe 11 Zuwa 12:30 Na Ranar Zaɓe

    INEC ta dage zabe a rumfuna 10 a jihar Legas

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

No Result
View All Result

El-Rufa’i Ya Ba Mara da Kunya, Daga Imam Murtadha Gusau

Mohammed LerebyMohammed Lere
September 24, 2019
in Ra'ayi
0
Capital School

Capital School

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin kai

Assalamu Alaikum

Ya ku ‘yan uwana ‘yan Najeriya masu girma, masu daraja! Wallahi, Allah ya sani, kuma shine shaida, na dade ina kwakkwaran bincike da kuma bibiyar ayukka da tsare-tsare, da salon mulki irin na gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagorancin mai girma adalin gwamna, masoyin talakawa, mai kaunar kawo canji na gaskiya a cikin al’ummah, wato Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i; sai daga karshe sakamakon bincike na ya tabbatar mani da cewa, lallai wannan mutum alkhairi yake nufi ga jihar sa ta Kaduna da kuma kasar nan baki daya. Na gano cewa wannan gwamna wallahi, wallahi, wallahi, talaka ne a gaban sa ba aljihun sa ba, kuma na gano, burin sa shine, yaya za’a yi a gyara tsarin kasar nan, ta dawo kamar yadda ake tafiya a can da, ya zamanto babu banbanci tsakanin dan mai kudi da dan talaka; tsakanin ‘ya ‘yan masu mulki da ‘ya ‘yan wadanda ake mulka.

Imam Murtada Gusau
Imam Murtada Gusau

Ya ku bayin Allah! A kasar nan ta mu mai albarka Najeriya, mun dade muna ta kiraye-kiraye zuwa ga gwamnati da dukkanin wani mai ruwa da tsaki a harkar ilimin kasar, cewa, wallahi idan ana so ilimin kasar nan ya gyaru, ya koma mai inganci kamar can da, inda da dan Sarki da dan gwamna da dan attajiri duk ajin su daya, to sai an cire son zuciya, ya zamanto an rusa duk wani tsari na makarantu masu zaman kan su (private schools), ko kuma a rage yawan su, abar masu inganci daga cikin su, sannan ya zamanto duk wani mai hali, da ‘yan siyasa, da manyan jami’an gwmnatoci, da sarakuna duk su kai ‘ya ‘yan su makarantun gwamnati tare da ‘ya ‘yan talakawa, kamar yadda tsarin karatu yake a can da. Wannan hanyar ce kadai idan Allah ya taimake mu, sai tsarin ilimin mu ya gyaru. Amma matukar aka ce makarantun ‘ya ‘yan manya daban, na ‘ya ‘yan talakawa daban, to wallahi har abada harkar ilimin mu ba za ya taba gyaruwa ba, wannan ita ce gaskiyar magana.

Idan zamu tuna a shekarar 2015, lokacin da ake Kamfen din neman kuri’un talakawa, gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya dau alkawari, ya bayyana cewa idan Allah yasa yaci nasara, zai sa dan sa a makarantar gwamnati tare da ‘ya ‘yan talakawa.

Tun a wancan lokacin ‘yan adawa da sauran jama’ah suke ta ganin cewa gwamna El-Rufa’i ya fada ne kawai amma sam ba zai iya yin haka ba, saboda lalacewar makarantun gwamnati a kasar nan.

Sai ga shi ranar litinin, 23 ga watan Satumba 2019, a lokacin da aka bude makarantu, bayan hutun karshen zango da aka tafi, mai girma gwamna El-Rufa’i ya ba mara da kunya, ya cika alkawari, ya garzaya da dan sa na cikin sa, Abubakar Al-Sadiq mai shekaru shida (6), zuwa makarantar gwamnati ta Kapital School da ke Kaduna, kamar yadda yayi alkawari a can baya, a inda aka yi masa rajistar shiga aji daya; kuma yayi kira ga sauran jami’an gwamnati da ‘yan siyasa da su yi koyi da shi, su sa ‘ya’yan su a makarantun gwamnati kamar yadda yayi, domin ta nan ne kadai hanyar da ‘yan siyasa da hukumomi za su bi suyi hobbasa domin inganta ilimi.

Sannan kamar yadda kowa ya sani ne, tun bayan hawan gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i kujerar mulkin Kaduna ya fara aiki tukuru wajen ganin cewa ya gyara makarantun jihar, wanda a halin yanzu aka kusa kammalawa da yardar Allah.

Sanadiyyar kokarin sa, an samu karin dalibai masu shiga makarantu a fadin jihar, da kuma karin daukar malamai kwararru da yayi.

Da wannan ne nike cewa a gaskiya Allah ya taimaki jama’ar jihar Kaduna da zakakurin shugaba, jarumi, kuma adali, mai kishin talakawan sa. Ina rokon Allah yaci gaba da taimakon sa, da yi masa jagora, akan irin wadannan namijin kokari da yake yi wa jjhar sa, sannan ina rokon Allah ya ba shi ikon dare wa kan karagar mulkin Najeriya baki daya, domin irin wadannan shugabannin ne kasar nan ta ke bukata a halin yanzu; wadanda za su sa gaba wurin ganin talakawa sun ji dadi. Allah ya taimake shi, yayi masa jagora, amin.

Ya ku ‘yan uwana! Idan za ku iya tunawa, a shekarun baya, mutanen jihar Kaduna sun fada cikin rudani sanadiyyar yawan barkewar rikice-rikice da tashe-tashen hankula a jihar, musamman a wurare irin su Kasuwar Magani da sauran su; rikicin da yake yin sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama da kuma dukiyoyin su; sannan ga garkuwa da ake yi da mutane domin karbar kudin fansa, ga rashin zaman lafiya da aka yi fama dashi a fadin jihar, wanda yasa mutane da dama sun fada cikin dimuwa da fargaba a wadancan lokuttan.

Cikin taimakon Allah, mai girma gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya tashi tsaye haikan, da yake Allah ya dubi kyakkyawar niyyar sa, sai ya taimake shi, ya kawo karshen wadannan rikice-rikice.

Sanadiyyar Allah ya azurta jihar Kaduna da jarumin gwamna, marar tsoro, wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye don ganin rikici a jihar bai fi karfin gwamnati ba kamar yadda yakan faru a da can baya, da sai an yi dimbin kashe-kashe, an kona gidaje da dakunan Ibadah kafin a kawo wa mutane dauki, wannan karon gwamna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i yayi namijin kokari da tsayuwar daka, wurin ganin hakan bai sake faruwa ba da ikon Allah da taimakon sa.

Da kansa ya rika fita titunan jihar, kwararo-kwararo, sako-sako, lungu-lungu, kauye-kauye, karkara-karkara yana kokarin tabbatar da ganin ana bin doka da oda, sannan kuma mutane basu dauki hukunci da doka a hannun su ba.

Ya ku ‘yan Najeriya! Lallai, babu shakka, irin wannan salon gudanar da mulki irin na mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i, ya nuna cewa, shi ya cika gwani kuma abin alfaharin kowa, duba da yadda ya tabbatar da cewa, ya zama zakaran gwajin dafi cikin takwarorin sa gwamnoni, kuma garkuwa ga al’ummar sa ta jihar Kaduna.

Tun bayan rantsar da shi a karon farko, da shigar sa Ofis, a shekarar 2015, a matsayin zababben gwamnan jihar Kaduna, karkashin tutar jam’iyyar APC, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya tarar da jihar cikin kangin fatara da talauci gami da tabarbarewar al’amurran tsaro, da na ilimi, hadi da kiwon lafiya, biyo bayan kura-kurai da tabargazar da gwamnatocin baya suka tafka. Amma cikin hanzari da himma, mai girma gwamna ya sanya kaimi domin magance dukkan matsalolin da suke addabar jihar.

Cikin wadannan shekaru, duk wanda yasan Kaduna, wallahi yasan cewa mai girma gwamna ya samu gagarumar nasarar ciyar da jihar Kaduna gaba ta fannoni daban-daban, sai fa idan mutum ya kasance shi dan adawar siyasa ne, to anan irin wadannan kuwa ba za su taba ganin gaskiya ba balle har su bi ta. Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya bayar da gudummawa sosai a wurare da dama, misali:

1. Fannin Tsaro

2. Fannin Ilimi

3. Fannin Tattalin Arziki

4. Fannin Kiwon Lafiya

5. Fannin Siyasa

6. Rikicin Fulani Da Makiyaya da sauran su.

Haka zalika, duba da nagartar sa, da kuma irin ayyukan alkhairin da ya shuka a jihar sa, yasa mai girma shugaban kasa, Alhaji Muhammadu Buhari ziyartar jihar sau da dama domin kaddamar da ayukka tare kuma da yaba masa kan yadda yake kokari wurin tabbatar da zaman lafiya da hadin kan ‘yan jihar.

Duk wadannan batutuwa, kadan ne na zazzakulo maku daga kowane fanni da mai girma gwamna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya tabo cikin shekarun da yayi yana jan ragamar mulkin jihar Kaduna. Domin wannan shafi yayi kadan matuka wurin iya zayyano komai a cikin lokaci guda.

Shakka babu, gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i ya cika jarumi kuma gwarzon namiji, kuma ya cika shugaba nagari abin koyi. Don haka ina ganin ya zama dole in yaba wa wannan jajirtacce, gwani, zakaran gwajin dafi cikin takwarorin sa gwamnoni, kuma abin alfaharin talaka, wanda ya cancanci ya jagoranci kasar nan zuwa tudun-mun-tsira da yardar Allah!

Duba da wannan, yasa nike ganin cancantar ‘yan Najeriya su tashi tsaye gaba dayan su, da rokon Allah da addu’o’i, domin ganin cewa Allah yasa wannan bawan Allah ya zama shugaban kasar Najeriya, domin kowa yaji dadi, ya amfana! Ya Allah ka amsa muna, amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa ta adireshi kamar haka: ko kuma 08038289761.

Tags: Abubakar Al-SadiqGwaniHausajajirtacceNasir Ahmad El-Rufa'iPREMIUM TIMESRa'ayi
Previous Post

Sabon rikici tsakanin gwamnati da kamfanonin wutar lantarki ya tirnike

Next Post

ZABEN 2019: Atiku ya garzaya Kotun Koli

Next Post
Atiku and Buhari

ZABEN 2019: Atiku ya garzaya Kotun Koli

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Abubuwa 11 da ake so a yawaita yi a watan Ramadan
  • ZABEN KADUNA: PDP ta yi murdiya a wasu kananan hukumomi, zan Kalubalance su a Kotu – Uba Sani
  • SABUWAR ƁARAKA A PDP: An dakatar da Fayose, Anyim, Gwamna Ortom zai gurfana gaban kwamitin ladabtarwa
  • Yunƙurin ‘yan majalisar APC uku masu so a halasta tu’ammali da tabar wiwi ya samu cikas
  • ZAƁEN SHUGABAN ƘASA: Keyamo ya roƙi SSS su kama Obi da Datti, saboda furucin cewa ‘zaɓen 2023 daidai ya ke da mulkin soja’

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.