Rundunar ‘Yan sanda na jihar Kano ta kama rikakkun barayi, ‘yan taadda

0

A wani buki da yayi kama da na baje koli amma wannan karon ba baje kolin kayan alatu ba rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta baje kolin wasu rikakkun barayi ne, ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da ‘yan sara suka da suka addabi mutane.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Ahmed Iliyasu ne ya baje wadannan ‘yan ta’adda a bainar manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan dake Kano.

Iliyasu ya ce an kama duk wadannan batagarin a cikin kwanaki 20 da suka wuce.

Yace baya ga masu garkuwa da mutane da aka kamo, ankamo ‘yan daba dake farautar mutane suna kwace musu wayoyi, sannan da rikakkun barayi ‘yan fashi da makami da kuma yara masu satan kudaden mutane a yanar gizo, wato Yahoo-Yahoo.

” Ranar 15 ga watan Agusta mun kama wani mai suna Abubakar Ibrahim a garin Kaduna, da manya-manyan kullin tabar wewe, da wani Harrison Ofesi shima a Kaduna dake harkar saida ganyen tabar wewe buhubuhu. Shi Harrison har da motar sata aka kwato.

” Mun kama wasu masu garkuwa da mutane hudu, da suka yi ta kokarin yin garkuwa da wani Sani da matarsa a kwatas din Gwaron Dutse dake Kano.

” Sannan zaratan ‘yan sandan Puff-Adder tare da hadin guiwar ‘yan kungiyar Miyetti Allah na jihar Kaduna da Kano, sun kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane da wasu abokan aikinsa 4 a dajin Falgore da suka shahara wajen yin garkuwa da mutane da kuma aikata fashi da makami a manyan titunan jihohin.

An kwato komfutoci 4, ID card na sojoji da na ‘yan sanda, kayan sojoji, Gatari,takubba, barandami, fatefate, bindigogi kirar AK 47 da harsasai, kwalabe Kodin 125, dauri-daurin tabar wewe, wukake, baturan Sola, da wayoyin mutane da dama.

Share.

game da Author