MAI RABON GANIN BADI: Alhazai 550 sun tsallake rijiya da baya a hadarin jirgin ‘Max Air’ a Minna

0

Wasu Alhazai har 550 daga jihar Neja sun gamu da tashin hankali bayan jirgin saman Max Air da ya dauko daga kasar Saudiyya ya sauka da kyar a filin jirgin saman Minna.

Hassana Aliyu, wadda itace shugaban hulda da jama’a na hukumar Alhazan jihar Neja ta tabbatar da aukuwar hadarin jirgin a filin jirgin saman Minan.

Haka kuma kamar yadda wani da baya so a fadi sunan sa ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ce wannan tashin hankali ya auku ne a wajen karfe biyar na Asubahi.

” Jirgin ya nemi sauka amma abin ya gagara, hakan yayi ta kokarin sauka amma kuma bai yiwu masa ba shine kawai jirgin ya nausa kasa. Daga nan ne fa aka yi maza-maza aka rika fiddo da mutanen ciki jirgin daya bayan daya.

Wani shima ya ce lallai fa yau sun ga tashin hankali a filin Mina din.

Yace dole su yi wa Allah godiya ganin cewa kowa ya fito lafiya ” amma yau da ace wannan jirgi ya kama da wuta da sai ya babbake filin jigin kaf kafin a iya fito da Alhazan domin babu motan kashe gobara a filin jirgin saman nan kwata-kwata.

Daga baya shugabannin hukumar kula da filayen jiragen saman Najeriya sun garzayo maza-maza wannan fili domin ganawa akai.

Share.

game da Author