Adam Zango zai rika sakin fim dinsa a yanar gizo, YouTube

0

Fitaccen dan wasan Kannywood kuma Furodusa Adam Zango ya bayyana cewa daga yanzu zai rika sakin fina-finan sa ne ta yanar gizo wato a YouTube.

Ya ce zai rika sakin fina-finan sa ne a shafin sa na YouTube.

” Daga yanzu duka fina-finai na za a rika ganin su ne a shafina na YouTube.

Zango ya ce zai fara da fim dinsa na Gudun Mutuwa wanda zai saki ranar 10 ga watan Oktoba.

Sannan ya bayyana yadda duk masoyansa da masu sun kallon fina-finan sa zasu rika iya kallon fim dinsa a YouTube.

Da farko dai duk mai son kallon fim din Gudun Mutuwa zai aika da naira 1000 ne a asusun ajiya na baki da ya bayyana a shafin sa na Instagram ko kuma ka tura katin waya na dubu daya a wasu layukan da ya saka a shafin na sa.

” Idan mutum yayi haka, ranar da za a saka fim din Gudun Mutuwa za a tura masa wani link da zai yi amfani dashi wajen kallon fim din.

” Ina kira ga masoyana da su aiko da kudin su domin samun daman kallon fim din. Sannan daga yanzu zan rika sakin fina-finai na ne ta yanar gizo wato a YouTube.

” Yanzu dai ko muna so ko bama so barayin fina-finai sun kashe harkar fina-finai a kasuwannin mu. Ko kayi fim din ba za ka samu komai ba. Dole ne mu kirkiro hanyoyin da zamu rika siyar da fim din mu domin samun riba kuma mu iya shirya manyan fina-finai kamar takwarorin mu a duniya.

Sai dai kuma duk da yabawa wannan himma na Zango da wasu suka yi, Hassana Dalhat, mai sharhi akan fina-finan Hausa ta kara da cewa duk da dole a yaba wa wannan kokari na Zango sai ya dada inganta shi sosai.

” Mafi yawan masu kallon fina-finan Hausa basu da fasahar iya amfani da wannan kafa na YouTube. Wasu daga cikin su ma ba su san shi ba kuma suna da yawan gaske. Za a iya samun matsala wajen tallata wannan fasaha da zai yi amfani da wajen sakun fina-finan sa.

” Sannan kuma za bayan mutum ya biya naira 1000 dole sai ya nemi data da zai saka a wayarsa ko Komfuta sannan ya kalli fim din. Wannan ma zai iya zama matsala ga masu son kallon fina-finan.

Gudun Mutuwa fim ne da mutane suke ta muradin kallon sa. Fitattun yan wasa afim din sun hada da shu kansa Adam Zango, Falalu Dorayi, Halima Ateteh da Sukeiman Bosho.

Share.

game da Author