A ranar Talata majiya mai karfi ya sanar wa PREMIUM TIMES cewa sabon shugaban kamfanin mai na Kasa NNPC Mele Kyari ya fara yin tankade da rairaya a duka kamfanoni da hukumomin dake karkashin kamfanin mai wato NNPC.
A bayanan da ya iske mu kamfan NPDC da ke kula da kasuwanci da hada-hadar danyen mai ne wannan garambawul zai fi shafa.
Sai dai kuma ba a bayyana sunayen wadanda abin ya shafa ba zuwa yanzu, shugaban NNPC Kyari ya ce wannan garambawul ya zama dole a yi shi idan ana son a ci gaba sannan da gyara ayyukan matatar mai din.
A gajeruwar hira da yayi da PREMIUM TIMES, Kyari ya ce wasu sun maida NNPC din kamar shagunan su da gidajen su.
” Wasu manyan darektoci sun maida kamfanin NPDC kamar shagunan su ko kuma gidajen su. Sun maida ita kasuwa. Yadda suke so kawai suke yi. Su dibi can su raba nan. Sannan babu yadda aka iya da su.
” Ire-iren wannan harkalla dole a dakatar dashi haka sannan a saka sabbin hannu a wadannan wurare idna har ana so a ci gaba.
” Ba zan saka ido in bari wasu na yin abin da suka dama ba da dukiyar kasa. Yanzu kam idan dai a kamfanin mai na Kasa zaka yi aiki tog dole ka shiga taitayinka.
Bayan haka kuma tuni har hukumar NPDC ta rubuta wa kamfanonin hadin guiwa da ke aikin hako danyen mai a kasar nan wasikun gargadi cewa su maida hankali wajen samarwa mutanen kauyukan da kamfanonin su ke aiki ababen more rayuwa yadda ya kamata.
Sannan kuma da biyan haraji da kuma maido kudaden da duk ya kamata a aika su asusun gwamnati.
”