TOZARTA EKWEREMADU: Dole fa sai an rika taka wa IPOB burki – Jakadan Najeriya a Kasar Jamus

0

Harin da ‘yan kungiyar IPOB suka kai wa Sanata Ike Ekweremadu a Jamus “babban laifi ne kuma ta’addanci ne.” Haka Najeriya ta bayyana, tare da kalubalantar ‘yan sandan Jamus da su gaggauta gurfanar da su domin su fuskanci hukunci.

‘Yan kabilar Igbo ne suka ci masa mutunci, duka da kuma yaga masa riga, a lokacin taron bikin Kabilar Igbo a garin Nuremberg, Jamus.

Sai dai kuma ‘yan sandan kasar sun ce kawai masu zanga-zanga ne kimanin su 30 suka yi wa Ekweremadu zanga-zanga, dga nan kuma su jami’an tsaron suka yayyafa wa abin ruwa

A wata hira da wani dan jarida mai zaman kan sa, mai suna Rouna Meyer, wadda shi Meyer ya turo wa PREMIUM TIMES, Jakadan Najeriya a Jamus, Yusuf Tuggar ya bayyana cewa ba dqidqi ba ne ‘yan sanda ko ma wa ya kira abin da aka yi wa Ekweremadu da sunan zanga-zanga.

Cin fuskar da aka yi wa sanatan dai an yi ta nuna shi a soshiyal midiya, ana nuno IPOB na bin Ike a guje su na duka, mangari har da keta masa riga.

Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya dauki alhakin cewa IPOB ne suka kai masa harin, kuma a haka za su ci gaba da tozarta shugabannin Inyamirai a kasashen waje.

“Hukuma ta kalli bidiyon yadda aka ci mutuncin sa. Don haka duk mai kokarin canja wa tuwo suna har ya ce wai ba a doke shi ba, to ya na so ne kawai ya kawo wani sabon abu kawai. Ko kuma ya na da wata kullalliya.

“Ta ya za a ce zanga-zanga ce ta lumana, alhali kuma masu zanga-zangar sun rika bin sa su na duka. Duk inda aka yi haka a duniya, to laifi ne. tilas kuma sai an hukunta masu laifin.

Ekweremadu dai ya shafe shekara 12 rike da mukamin mataimakin shugaban majalisar dattawa.

Tugger ya ce abin da aka yi wa sanatan an yi niyyar ji masa ciwo a jiki.

“Kowa ya kalli bidiyon da aka bin sa a guje kamar dabba, ya na gudu ana kekketa masa riga.”

Daga nan sai ya kara cewa ya yi tunanin jami’an tsaro za su damke ‘yan IPOB. “Saboda wannan ba magana ce Sanata Ekweremadu kadai ba. Ya zama dole a kare rayuka da lafiyar kowane dan Najeriya.”

Saboda haka mu na son a rika mutunta ‘yan Najeriya a kwace kasa. Ya ka ke tsammani idan dan wata kasa ne a ka ci zarafi haka a Najeriya?

Daga nan sai ya ce su na jira su ga abin da mahukuntan Jamus za su yi da kuma matakin da za su dauka a kan mummunan lamarin.

Share.

game da Author