Jam’iyyar PDP ta ce lallai idan akwai abin da yake yi mata dadi game da zaben jihar Kogi da ke tafe ba zai wuce yadda APC ta tsaida gwamnan jihar Yahaya Bello dan takarar ta a zaben.
Kakakin jam’iyyar PDP na jihar Kogi Bode Ogunmola, ya bayyana cewa Allah ne ya amsa addu’ar PDP, APC ta tsaida Yahaya Bello domin kuwa fatafata da shi za su yi a zaben gwamnan dake tafe.
” Bama kyautata zaton akwai karamar hukuma koda daya ce tak da Yahaya Bello zai yi nasara a zaben gwamnan jihar da za ayi a watan Nuwamba.
” Su kansu mutanen jihar sun dandana kudar su tun bayan darewar Yahaya Bello kujerar gwamnan jihar. Ba sai an yi wa wani tuni ba. A dalilin haka kuwa nake so kowa ya sani cewa bamu da fargaba ko na kwabo a zaben gwamnan jihar da ke tafe.
” Idan ya iya bi ta kan shugabannin jam’iyyar sa da deliget har suka iya tsaida shi dan takarar su, ba zai samu haka ba a wajen mutanen jihar Kogi domin kowa ya shaida irin bakar wahalar da aka shiga a tsawon mulkin sa.
Saidai kuma a martani da darektan yada labaran gwamna Bello, Kingsley Fanwo, ya maida wa PDP din yace a shirye suke tsaf domin tunkarar zaben da ke tafe.kyma sune da nasara.
” Ba mu shakkan komai kuma a shirye muke domin tunkarar wannan zabe da ke zuwa. Gwamna Bello ba zai ce komai ba tukunna saidai sakamakon zabe ne zai tabbatar da ko waye zai cira tuta bayan haka, wadda APC ce zara yi nasara.
Discussion about this post