ATIKU KO BUHARI: Kotu ta wanke jami’an tsaro daga zargin magudin zabe

0

A ci gaba da gwagwarar shari’ar da ake yankewa a yau Laraba, Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da zargin da PDP ta yi wa jami’an tsaro cewa sun yi magudi, domin Shugaba Muhammadu Buhari ya kayar da Atiku Abubakar a zaben 2019.

Kotun ta yi watsi da wani bangare da PDP ta yi zargin cewa APC ta yi amfani da jami’an tsaro, inda suka hada kai suka yin walle-walle da zaben shugaban kasa na 2019.

Idan ba a manta ba, PDP ta zargi shugaba da ke kai, Muhammadu Buhari cewa shi da manayan hukumomin gwamnati da INEC din ita kan ta da kuma jami’an tsaro na da hannu wajen karkatar da zabe da kuma sakamakon zabe, domin Buhari ya yi nasara a kan Atiku.

Kotu a yau Laraba ta samu cikar a cikin korafin da PDP ta gabatar, yayin da INEC ta nuna wa kotu cewa kamata ya yi PDP ta bayyana sunayen jami’an tsaron da ta ke zargi a cikin karar ta da shigar.

Don haka kotu ta cire jami’an tsaro daga cikin wadanda ake zargi. Ana nan ana ci gaba da karanto bayanan shari’a kafin a yanke hukunci.

Share.

game da Author