Yadda aka yi musayar kamammu tsakanin Gwamnatin Katsina da ‘yan bindiga

0

Gwamnatin Jihar Katsina ta damka wa ’yan bindiga wasu da aka kama bisa zargin garkuwa da mutane su tara.

Yayin da su kuma ‘yan bindiga suka mika wa Gwamnatin Katsina wasu mutane biyar da ke a hannun su, bayan sun yi garkuwa da su.

Daraktan Yada Labarai na Gwamna Aminu Masari, mai suna Abdu Labaran, ya ce gwamnatin Masari ta sake ‘yan bindigar ne domin su ma a na su bangaren su sake sako wasu mutanen da ke hannun su.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin da aika-aikar hare-haren masu garkuwa da mutane ya yi muni sosai a kasar nan.

Kwanan nan ne jihar ta cimma yarjejeniyar ajiye makamai da kuma daina sace mutane ana garkuwa da su, ita da mahara.

“ An fara wannan zaman tattaunawa ne a Dajin Rugu tsakanin gwamnatin Katsina da ‘yan bindiga, wadanda suka addabi kananan hukumomi takwas a fadin jihar.

“Wannan yarjejeniya ta fara cimma nasara, tunda ga shi har sun saki mutane 5, su kuma an mika musu tara.”

Sanarwar ta ce an yi musayar ce a cikin Gidan Gwamnatin Jihar Katsina, a gaban Gwamna masari da dukkan manyan jami’an tsaron jihar da kuma wakilai biyu daga ‘yan bindiga, wadanda dama a baya su ne suka dauki alkawari a gaban gwamnan.

Da ya ke magana, Gwamna Masari ya ce ‘yan bindigar za su sake sakin wadansu 29 da suka yi garkuwa da su, tun a jiya Talata din.

Ya ce “za a ci gaba da haka har nan da kwanakin da mahara za su saki dukkan mutanen da ke hannun su, su kuma jami’an tsaro za su daki dukkan ‘yan bindigar da ke hannun su.”

Masari ya ce a tsarin yarjejeniyar, mahara za su rika sakin wadanda su ka kama, tare kuma da damka bindigogin da ke hannun su a hunnan jami’an tsaro.

Share.

game da Author