A ci gaba da gwagwagwar karanta shari’a da Kotun Daukaka Karar Zaben Shugaban Kasa ke yi, kotun ta yi watsi da ikirarin da INEC ta yi cewa karar da PDP ta shigar dangane da satifiket din Shugaba Buhari, batu ne na kafin zabe, ba bayan an rigaya an yi zabe ba.
INEC ta ce batun satifiket din bai kamata ya shigo a cikin wannan kara ba, kamata ya yi a ce tun kafin zabe PDP ya kamata ta kai batun kutu.
PDP ta tsaya kai da fata cewa Buhari bai cancanci tsayawa takara ba, domin ba shi da takaitaccen satifiket din da doka ta tanadar ya tsaya takarar shugaban kasa da shi.
Wannan na daga cikin batutuwa da yawa wadanda PDP ta yi amfani da su ta maka INEC, Buhari da APC kotu.
Sai dai shi kuma Shugaban Kotun, ya yi amfani da Sashe na Doka na 138 (1) (a) ta Dokar Zabe, inda ya ce sashin ya amince mai kara ya shigar da karar zargin abin da ya danganci gabatar wa INEC bayanai na karya.
“Don haka na amince da cewa wannan batu ba batu ba ne da ya tsaya a kana bin da ya danganci shari’ar abin da ya faru kafin zabe ba ne kawai.”
Garba ya ce don haka kotu za ta duba sahihanci ko akasin abin da ake kara akai.
Duk sauran alkalai hudu ba su yi tantamar wannan bayani ba.