Sowore zai ci gaba da zama a tsare – Hukuncin Kotu

0

Alkalin babban kotu dake Abuja Nkeonye Maya yayi watsi da karar da babban lauya Femi Falana ya shigar yana kalubalantar tsare Yele Sowore da SSS ke yi.

Idan ba a manta ba jami’an SSS sun cafke Sowore bisa dalilin kokarin shirya gangamin na gudanar da zanga-zanfga a fadin kasar domin nuna gazawar gwamnati mai mulki wajen samar da tsaro da ababen more rayuwa ga ‘yan Najeriya.

Kotu ta ba SSS damar tsare Sowore tsawon kwanaki 45

Kakakin runndunar Peter Afunanya, ya bayyana cewa hukumar ta gano cewa Sowore yana tattaunawa sannan da ganawa da wasu mutane a wasu kasashen waje domin wannan gangami da ya sa a gaba da hakan ya sa dole a taka masa burki domin kada ya kawo rudani a kasar nan.

Bayan nan sai kotu ta yanke hukunce a tsare Sowore har na kwanaki 45 wanda hakan ya sa lauyan Sowore, Femi Falana ya garzaya kotu domin kalubalantar wannan hukunci na kotu.

Sowore da Kanu sun yi shirin kifar da gwamnatin Buhari –SSS

Sai dai kuma hakar sa bai cimma ruwa ba domin babban kotu ta yi watsi da wannan kara da ya shigar.

Bisa ga hukuncin da alkali Nkeonye Maya ya yanke ranar Laraba, Sowore zai ci gaba da zama a tsare har sai wa’adin kwanakin da aka kotu ta dibar masa ya cika.

Share.

game da Author