Akalla kashi 30 bisa 100 na yara kanana basu makarantar boko a jihohin Arewa Maso Yammacin Najeriya – UNICEF

0

Jami’i a Asusun tallafawa kananan yara na majalisar dinkin duniya, (UNICEF) Muntaka Muktar ya bayyana cewa sama da kashi 30 bisa 100 na yara kanana a jihohin dake Arewa Maso Yammacin Najeriya basu makarantar boko, banda jihar Kaduna.

Muktar ya fadi haka ne a wani taro da Asusun UNICEF ta shirya domin tattauna matsalolin dake hana yara kanana shiga makarantun boko da aka yi a jihar Kano ranar Talata.

Ya ce jihohin dake yankin sun hada da Kano, Katsina, Sokoto, Zamfara da Kebbi amma sai dai wannan matsala bai shafi jihar Kaduna ba.

“Ilimin firamare kyauta ne kuma dole ne ga yara kanana saidai bisa ga sakamakon bincike da aka gudanar ya nuna cewa yara akalla miliyan 10.5 masu shekaru 5 zuwa 14 basa makarantar boko a Najeriya.

“ Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa yara kashi 61 bisa 100 masu shekaru 6 zuwa 11 da yara kashi 35.6 bisa 100 ‘yan watanni 36 zuwa 59 ne ke zuwa makarantar boko a Najeriya.

Mukhtar ya kuma ce rashin saka ‘ya’ya mata a makarantun boko ya fi yawan gaske a yankin Arewa Maso Yamma da Arewa Maso Gabas.

A yankin Arewa Maso Yamma adadin yawan ‘ya’ya matan da basa makaratar boko sun kai kashi 47,3 bisa 100 sannan a Arewa Maso gabas sun kai kashi 47.7.

Ya ce rashin saka yara musamman ‘ya’ya mata a makarantun boko a Arewa na da alaka ne da talauci da wasu al’adu na mutanen yankin da wasu har yanzu basu jefar ba.

Mukhtar yace koda yake UNICEF ta na ta kokarin wayar da mutane sanin mahimmancin saka ‘ya’yan su a makarantun boko, rashin gyara makarantun na maida musu hannun agogo baya.

“A dalilin haka ya sa da dama ke gararamba a titunan kasarnan ba tare da iyayen su sun tura su makarantu ba.

Ya kara da cewa yanzu fa baya ga tallafi da UNICEF din ke badawa suna bi suna gina ajujuwa a makarantu da gyaran wadanda suka lalalce domin yara.

Mukhtar ya yi kira ga gwamnatocin jihohi da su yi amfani da wannan tallafi na UNICEF domin inganta fannin ilimi a jihohinsu.

Share.

game da Author