Sowore da Kanu sun yi shirin kifar da gwamnatin Buhari –SSS

0

Jami’an Tsaro na SSS sun kalubalanci hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta zartas, inda ta umarci SSS din su tsare dan taratsi Omoyele Sowore tsawon kwanaki 445, maimakon kwanaki 90 da SSS din suka nemi kotun ta ba su iznin tsare shi har kafin a kammala bincike.

SSS sun nuna wa kotu cewa binciken da suka fara ya tabbatar musu da cewa “RevolutionNow’’ da Sowore ya kafa, sabubba ne da ya kitsa shi da wasu abokan shirin sa “domin kifar da gwamnatin Najeriya.”

Dalili kenan SSS suka ce akwai yiwuwar su sake garzayawa kotu omin karin kwanakin da za su ci gaba da tsare Sowore, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar AAC a zaben 2019, kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters.

Haka dai daya daga cikin jami’an SSS, Godwin Agbadua ya bayyana a rubuce ga kotun, a madadin Hukumar SSS.

Ya ce Sowore ya yi amfani da shafin yanar gizo da ya sa wa suna RevolutionNow domin makarkashiyar kifar da zababbiyar gwamnatin dimokradiyya.

“Sowore ya yi basaja ne da cewa wai zanga-zanga za su yi, domin yaudarar jama’a su bi zugar su har su kifar da gwamnati.”

“Haka nan kuma mun gano yadda ya rika yin tarukan sirri da mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB domin hada kasaitacciyar rundunar masu zanga-zangar shirin kifar da gwamnati.”

SSS sun ce Nnamdi Kanu ya karbi tayin Sowore hannu bib-biyu tare da shirya yadda za su rika kai hare-hare a kasar nan.

“Sowore ya rika yin taro da wasu abokan shirin sa a kasashen Amurka da Dubai, inda aka ba shi milyoyin daloli domin kifar da gwamnati da kuma kokarin kwato Sheikh Ibrahim El-Zakzaky daga hannun jami’an tsaro. Har da wasu ‘yan haramtacciyar kungiyar IMN ya rika yin taro.” Inji SSS.

Share.

game da Author