Mai Shari’a Taiwo Taiwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya bai wa jami’an tsaron SSS ikon ci gaba da tsare dan taratsi Omoyele Sowore har tsawon kwanaki 45.
Taiwo ya ce a ci gaba da tsare Sowore saboda ana zargin sa ne da furuci na yi wa gwamnati zagon kasa.
Hukumar DSS ce da kan ta ta garzaya kotu ta nemi a ba ta iznin ci gaba da tsare Sowore, bayan da ya shafe mako guda a tsare a Hedikwatar SSS din da ke Abuja.
Mai Shari’a Taiwo ya zartas da hukuncin amsa rokon da SSS suka yi ne a wani hukunci na kai-tsaye da ya yanke, ba tare da bayar da dama lauya mai kare Sowore ya tsaya masa a madadin sa ba.
Ya ki yarda da lauya ya tsaya a madadin wanda ake tuhumar ne, saboda kamar yadda alkalin ya fada, laifi ne da ya shafi zagon kasa ga gwamnatin dimokradiyya.
Duk da dai SSS sun ce ba su kai ga samun wasu hujjoji ba, sun nemi da a ba su iznin ci gaba da tsare shi har tsawon kwanaki 45, wato daga ranar 3 Ga Agusta har zuwa ranar 21 ga Satumba mai zuwa kenan.
Mai Shari’a Taiwo ya ce za a ma iya sabunta ci gaba da tsare shi idan wadannan kwanaki 45 suka cika, matsawar hakan ta kama.
Taiwo ya ce ya bada iznin tsare Sowore ne ba tare da gurfansr da shi kotu ba, a bisa Doka ta 27(1) ta aikata zagon kasa ga gwamnati.
An kama Sowore a ranar 3 Ga Agusta, kwanaki biyu kafin gudanar da zanga-zangar gangamin game-garin da ya shirya, wadda ya sa wa suna #RevolutionNow, wato #JuyinTuruYanzu.
Wannan yunkuri ne gwamnatin Shugaba Muammadu Buhari ta yi kokarin kifar da zababbiyar gwamnati ce.
Discussion about this post