Dan tsohon gwamnan jihar Kogi Yarima Abubakar Audu Almustapha Audu ya bayyana cewa shugaban Jam’iyyar APC ne da kansa ke kulla masa tsiya domin kada a bashi takara gwamnan jihar Kogi a inuwar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.
Audu ya fadi haka ne a hira da yayi da PREMIUM TIMES inda yake cewa da gangar ne Oshiomhole yake shirya masa tuggu domin kada jam’iyyar ta tsaida shi dan takarar ta.
” Idan jam’iyyar APC na neman kudi sukan garzayo wuri in basu ko nawa ne amma yanzu da ya kai ga za muyi takara, kiri-kiri suna yi mini kumbiya-kumbiya har sun zare sunana sunce wai ban cancanci takara ba.
” Da farko kwamitin tantance ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC sun ce wai suna na da na rubuta a Fom din neman tsayawa takara ya nuna Almustapha Audu amma kuma a takardu na an rubuta Mustapha Audu ne. Banga inda haan ya zama dalilin da zai sa ace wai hakan yaza ma sanadi na kin amincewa da neman takarana ba.
” Sannan kuma wai ban saka takardar shaida ranar haihuwa na ba, bayan kuwa da kai na nsaia mika takarda cikin takardun da na mika wa hedikwatar jam’iyyar. Kuma ma har daukar bidiyo na yi domin shaida.
Al-Mustapha ya ce sai dai kuma ya na sa ran cewa kwamitin da aka nada domin sauraren korafin ‘yan takara zai yi masa adalci.
” Kuma ina so in tabbatar muku cewa idan ma kwamitin ta ki amincewa da korafi na zan garzaya ne kai tsaya ne sai kotu domin bin hakkina. Sannan kuma game da dan-uwana da muke takara a jam’iyya daya, babu komai muna nan tare a matsayin ‘yan uwa kuma hakan ba shine farau ba da ‘yan uwa za su fito takara a jam’iyya daya.
” Game da shugaban jam’iyyar mu Adam Oshiomhole kuwa rabon da inganshi ya kai watanni tara. A duk lokacin da ana bukaci in gana da shi sai ya ki. Ko a wannan mako, na tafi ofishin sa domin in ganshi amma duk da yana ciki kiri-kiri yaki amincewa in ganshi. Haka na gaji da zama na na kara gaba.
Akarshe, Mustapha ya ce koda anyi wannan zabe da ‘yan takara, shine zai yi nasara kuma kowa ya sani domin zai cinye duka ya bar musu sauran su raba a tsakanin su ‘yan takaran.
A martani da jam’iyyar ta maida wa Mustapha tace ya mika mata wasu takardun sa da ba su yi daidai da gaskiyan bayani akan sa ba.
” A takardar haihuwar sa ya nuna an haife sa a shekarar 1959 amma a fasfon sa ya nuna 1960. Tun a nan muka gano cewa akwai matsala. Hakan duk na daga cikin dalilan da ya sa muka ki wanke shi.