Shugabannin Igbo basu ga komai ba tukunna, saura gwamnoni – Inji Kanu

0

Shugaban kungiyar fafutikar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu ya bayyana cewa abinda aka yi wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu wanda dan kabilar ne a kasar Jamus soman tabi ne ga shugabannin Inyamirai.

Ya ce duk wani jigo dan kabilar Igbo ya kwana da shirin tasa ta kare musamman gwamnonin yankin saboda da su ake hada baki ana ci ya Inyamirai mutunci a Karkashin mulkin Buhari.

Kanu ya ce tuni har kungiyarsa ta saka kudi har naira miliyan daya ga duk wanda ya sanar wa kungiyar shirin wani gwamna da zai fita zuwa kasar waje. Idan ya gaya musu fitar gwamnan da kasar da ya tafi zai samu kyautar zunzurutun kudi har naira miliyan 1.

Yace sanata Abaribe ne kawai zai tsira daga farautar su saboda haka kowa ya kwana da shiri.

A cikin jawabin da yayi na fiye da awa daya, Kanu ya ce sune suka hada baki da gwamnatin tarayya aka haramta kungiyar.

” Sannan kuma suna gani aka zo har gida aka ci min mutunci. Baya ga haka sun bari Fulani makiyaya sun yi raga-raga da yankin Kudu maso Gabas basu ce komai ba.

” Wani abin ban haushi da takaici shine yadda gwamnonin yanki Inyamirai suke mara wa shirin RUGA ga Fulani da gwamnatin tarayya ta kirkiro baya.

Cin mutuncin Ekweremadu

A ranar Asabar ne tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu ya sha dukan tsiya a wajen ‘yan uwan sa Inyamirai a kasar Jamus.

Ekweremadu ya ziyarci Jamus ne domin halartar taron ‘Yan kabilar Igbo mazauna kasar Jamus.

Isar Ekweremadu wannan wurin taro ke da wuya sai ‘Yan uwan sa Inyamirai suma haushi da ihu suna zagin sa.

Da yayi kokarin shiga dakin taron sai ko suka hau shi da duka suka jawo shi waje da karfin tsiya suka yaga masa riga.

Kamar yadda Ekweremadu ya fadi a shafinsa na Facebook, ya ce yan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ne suka far masa a kasar Jamus.

” Na yi kokarin in yi musu bayani amma suka ci mini mutunci. Basu san irin kokarin da nayi bane wajen ganin shugaban IPOB Nnamdi Kanu, da sama masa beli.

Share.

game da Author