Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
‘Yan uwa na masu girma! Daga cikin manyan mu masu albarka, kuma tsoffin shugabannin kasar nan ta mu mai albarka, wato Najeriya, Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), shine shugaban da aka taba samu ya aikata ayyukan alkhairi, masu amfani ga al’ummah har sama da guda dubu daya a zamanin mulkin sa da yayi na shekaru takwas. A inda ni dai a iya sani na, bayan Shugaba Babangida din, babu wani Shugaba guda daya tak duk tarihin nahiyar Afirka, da tarihin Shugabanni da su ka ta ba yin hakan. Kai ko da Shugabannin da suke kan kujerar shugabancin kasashen su a halin yanzu, ban ji wani wanda ya kwatanta hakan ba, idan dai ba Gamji Dan kwarai, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ba. Wanda ya gina kuma ya samar da ayyukan alkhairin da ba su kirguwa a fadin yankin Arewa; Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), daya kenan daga cikin ayyukan Sardauna da muke amfana da su har yau. Sai kuma wasu ayyukan da yawancin su Gwamnonin mu na Arewa goma sha tara sun yi watsi da su, inda hakan yasa suka balbalce, yayin da suka sayar da wasu; irin su Babban Bankin Arewa, wato Bank of the North!

Kadan daga wasu ayyukan alkhairin IBB
Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), shine ya gina fadar mulki ta Shugaban kasa da ke babban Birnin Tarayyar Najeriya, wato Aso Rock Villa Abuja, kuma shine ya fara tare wa a cikin ta. Shine ya samar da gine-gine masu amfani a babban Birnin Tarayya, wato Abuja, kamar: Eagle Square, Federal Secretariat, FCDA Secretariat, National Mosque, National Church, National Assembly, Supreme Court, Court of Appeal, Barikin sojoji har guda goma a Abuja, Kasuwar Wuse, NNPC Tower.
Sannan kuma Shugaba Babangida shine ya samar da ma’aikatu masu matukar muhimmanci da har yau ake cin ribar su da amfanin su, irin su: NAFDAC, DIFRRI, MAMSER (NOA), CCT, CCB, CCN, Gifted Children’s School Suleja, NHIS, NEXIM, NDIC, NDLEA, FRSC, ECOMOG, Ministry of Women Affairs, NWC, National Mathematical Center, NDE, Ministry of Agriculture and Rural Development, NAFSESS, NSFCP, FUMTP, NPB, FEPA, NALDA, CDS, RMRC, CMEWS, NEPC, FMIDS, Petro-Chemical Plant Kaduna, Petro-Chemical Plant Eleme, Osaka Dam Ajaokuta, Shiroro Hydro Power Station Niger, Dukkanin Sakatariyoyin Gwamnatocin Jihohin Najeriya, da kuma dukkan sakatariyoyin da yanzu haka ake amfani da su a kowace karamar hukuma, sai Delta IX Gas Turbine Plant da tagwayen hanyoyin Abuja zuwa Kano, da hanyoyi masu tarin yawa da ba zai yiwu a fade su ba a dan wannan rubutu takaitacce.
Sannan Shugaba Babangida bai taba sayo tataccen man fetur daga wata kasar waje ba. Duk man fetur din da aka sha a zamanin mulkin sa, a matatun man da Nijeriya ke da su aka tace shi. Kuma a lokacin sa duk matatun man Nijeriya suna aiki dari-bisa-dari, haka ya sauka daga kan mulki ya bar su!
Sannan Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ne ya kirkiro sabbin Jihohi guda goma sha uku, a duk fadin Nijeriya don talaka ya amfana kuma ya san cewa ana mulki. A inda kafin hakan da kuma bayan hakan, babu wani shugaban Nijeriya da ya girmama talaka, ta hanyar kirkiro sabbin Jihohi da yawa haka domin talaka ya amfana, gwamnati ta zo kusa da shi.
Ga jerin Jihohin da IBB ya Kirkiro kamar haka:
1. Jihar Adamawa
2. Jihar Katsina
3. Jihar Jigawa
4. Jihar Yobe
5. Jihar Kebbi
6. Jihar Delta
7. Jihar Edo
8. Jihar Taraba
9. Jihar Kogi
10. Jihar Abia
11. Jihar Osun
12. Jihar Enugu
13. Jihar Akwa Ibom
Sannan Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida shine ya yawaita kananan hukumomi a Nijeriya, har yawan su ya kai 774. Sannan babu mamaki, kai da ke karanta rubutun nan a halin yanzu, idan ba domin hakan da IBB yayi ba, da watakila har yanzu Jihar ku babu ita a cikin jerin Jihohin Najeriya da muke da su yanzu. Sannan kuma da yanzu kana cikin wata karamar hukuma ne a jone. Amma sai ga shi saboda halin karimci da kishin ci gaban rayuwar ka, IBB din da babu mamaki mai yiwuwa har da kai ake zama ana zagin sa, ana cin mutuncin sa, ana maganganun da basu dace ba na batanci a gare shi. To ya kai bawan Allah, ka sani, ko-ka-ki ko-ka-so, shine dai mai kaunar ka tsakanin sa da Allah, tun da gashi nan ya kirkiro maku Jiha da karamar hukuma da kake cin gajiyar su da amfanin su a yau, wanda hakan ce ma ta baka damar samun bakin magana da babatu!
Sannan duk wanda ya san tarihin kasar nan, yasan da cewa Shugaba Ibrahim Badamasi Babangida ya bar Dalar Amurka kan farashin Naira goma sha takwas (N18). Sannan ba’a taba ganin dogon layin man fetur a gidajen mai ba, kai ko da kuwa sau daya ne, duk tsawon shekarun da yayi yana mulkin Najeriya.
Sannan shine Shugaban da ya fara samar da fanfunan tuka-tuka, wato Boreholes, a kauyukan da bututun ruwan fanfo wato Pipes din famfo ba su karasa ba.
Kuma har ila yau, a zamanin mulkin sa ne ‘yan Najeriya suka amfana da ruwan famfo a ko’ina, ba tare da wata wahala ba. Sai mutum ya bude, ya kunna yayi amfani da shi, idan ya gama sai yayi tafiyar sa, ya bar kan famfon a kunne yana ta zubar da ruwa a banza, saboda wadata da kuma irin yadda IBB din ya jajirce, ya tabbatar da ganin cewa ruwan famfon sun wadaci kowa da kowa, kuma sun shiga kowane lungu da sako na Najeriya.
Amma duk da wannan kokari da jajircewa da wannan bawan Allah yayi, wai a yau zaka samu wasu mutane suna zagin sa, suna suka tare da cin mutuncin sa. Ba domin komai ba sai don saboda son zuciya irin ta Dan Adam, ko domin saboda ya jahilci wannan bawan Allah, ko don an wanke kwakwalwar mutum, an yi masa karya da farfaganda cewa IBB mutumin banza ne. Wallahi ka sani ya kai bawan Allah, kana rage masa zunubai ne da wannan zagin naka mara dalili.
Eh, mun san da cewa IBB ajizi ne, mutum ne, Dan Adam ne kamar kowa, yana iya yin daidai kuma yana iya yin kuskure. Domin shi ba Annabi ba ne kuma ba Mala’ika ba ne ko wani katangagge ko ma’asumi daga aikata laifi ko kuskure. Amma dai ni nayi imani da Allah, ayyukan alkhairin sa sun fi na sharrin sa yawa!
Saboda haka, ina kira da muji tsoron Allah, mu girmama manyan mu. Kar mu yarda mu biye wa ‘yan kudu da wasu shedanun mutane da suke zagin wannan bawan Allah mai daraja da nagarta, saboda wata manufa ta su da suke bukatar cimmawa ta sharri. Alhali idan muka duba, zamu ga cewa ai su suna girmama nasu manyan. To don me kuwa za su rinka zuga mu mu muna cin mutuncin namu manyan?
Ina rokon Allah ya shirye mu, yasa mu gane, amin.
Shi kuwa tsohon Shugaban kasar Najeriya, wato Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), wanda ya cika shekaru saba’in da takwas da haihuwa, ina rokon Allah ya kara masa lafiya, imani da nisan kwana; kuma ya kara masa shekaru masu albarka da amfani ga Al’ummah, yasa ya gama lafiya, amin.
Ina rokon Allah ya zaunar da kasar mu Najeriya lafiya, ya taimaki Shugabanin mu, amin.
Dan uwan ku,
Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma 08038289761.