Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Lagos ta bayyana cewa rikicin da ya barke a unguwar Ile-Ekpo a tashar mota bai ci rai ko daya ba.
Kakakin Yada Labarai, Bala Elkamah ne ya bayyana haka a cikin wata takardar manema labarai da ya aiko wa PREMIUM TIMES.
Ya ce rikici ne tsakanin Hausawa masu tsintar bola da kuma ‘yan iskan gari da ake kira Awawa, wadanda matasa ne ‘yan kungiyar asiri.
Wannan rikici dai ya kai ga zama hargitsi, amma a ta bakin Bala, garzayawar da ‘yan sanda suka yi wurin cikin hanzari sun kwantar da hargitsin.
Ya ce tabbas wannan dauki da jami’an tsaro suka yi, ta hana rikicin ya watsu zuwa wasu yankuna.
Daga nan ya kara cewa har zuwa lokacin dai babu rahoton an rasa rai sanadiyyar rikicin. Sannan kuma ya ce ba su na kan binciken musabbabin tashin rigimar.
Amma kuma da yawan wadanda suka gani da idon su, sun shaida cewa mata ‘yan tireda sun tsallake sun bar kayan sana’ar su.
Haka su ma fasinjoji da direbodi da kwandastoci sun tsallake a guje kowa na gudun famfalaki.
An rika watsa hotunan kayan miya irin su tumatir, tattasai, attarugu da albasa wadanda aka yi fatali da su.
Shekaru 20 kenan daidai da yin rikici tsakanin Hausawa da Yarabawa a Shagamu, a Jihar Ogun inda aka yi asarar rayuka da dama.