Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi karin haske dangane da tattaunawar sirri da shugabannin majalisa su ka yi tare da Shugaba Muhammadu Buhari dangane da tsaron kasar nan.
Lawan ya ce ya gana da Buhari ranar Laraba, a Fadar Shugaban Kasa, tare da Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila.
Ya ce dukkan su sun amince cewa akwai matukar bukatar yin Taron Kasa a Kan Matsalar tsaro, wanda ya ce bangaren gwamnati za su gudanar da na su taro, su ma bangaren majalisa za su gudanar da na su daban.
Ya ce sun tattauna a kan neman mafita, inda a karshe dai suka amince cewa bangarorin biyu za su hada kai da kuma hada hannu domin gudanar da taron na kasa a kan matsalar tsaro.
“Hakan ya na da tasiri, saboda yayin da mu ke bayar da gudummawa ta bangaren sha’anin majalisa, ita kuma bangaren gwamnati ke ha alhakin gudanar da ayyukan da mu ka bijiro da su a karkashin doka.” Inji Lawan.
Wannan taron ganawa da suka yi, ya zo ne daidai lokacin da ake samun yawaitar kashe-kashen jama’a a fadin kasar nan, tare kuma da garkuwa da mutane a kowace rana.
Kididdigar PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa tsakanin watan Yuni da Yuni an kashe mutane akalla 500 a rikice-rikice daban-daban a kasar nan.
Yayin da kuma jama’a da dama ke ta kiraye-kirayen gwamnati da Shugaba Buhari su tashi tsaye domin gaggauta shawo kan munin rikicin, tun kafin ya faskara magancewa.