Buhari ya yi tir da Dattawan Arewa da suka yi kiran Fulanin Kudu su dawo gida

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya su yi watsi da kiraye-kirayen da Kungiyar Dattawan Arewa ta yi cewa Fulanin da ke zaune kudancin kasar nan, su gaggauta komawa Arewa.

“ Dukkan ’yan Najeriya na da ‘yancin zirga-zirga ko zama duk bangaren da suka ga dama a kasar nan.

Buhari yace kowace kabila na da damar zama inda ran ta ya kwanta mata, ko da ba a yankin ne asalin ta ba.

“ Kamar yadda Dokar Najeriya ta shimfida, gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari za ta ci gaba da kare dukkan al’ummar kasar nan a duk inda suka samu kan su da zama.

“ Babu wani da ke da ikon cewa wani ko wasu su fice daga wani bangaren kasar nan, kudu ko arewa, gabas ko yamma.” Cewar Buhari.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ya sa wa hannu, Buhari ya tambayi dalilin da zai sa irin wadannan dattawa masu kiran kan su shugabanni za su yi azarbabin shiga maganar da bai kamata su shiga su na bada gurguwar shawara ba.

“ Ba su iko ko iznin yin wani jawabi a madadin wani ko a madadin sauran al’umma.

“ Dattawan Arewa da sauran masu kiran kan su shugabannin kungiyoyi duk sun a wannan kasassabar maganganu ne a kan batun tsaron kasar nan don neman suna kawai.”

Daga nan sai ya kara da cewa dama kuma a fili ta ke cewa sun dade su na bata sha’anin zamantakewar siyasar kasar nan.

“ Kada a sake a ba su kofar da za su rika karkatar da jama’a, musamman Fulani makiyaya da suke kokarin yi wa romon-baka.

“ Gwamnatin Buhari na b akin kokarin ta wajen ganin an samu kawo karshen wannan rikici na Fulani makiyaya da kuma manoma a dukkan fadin kasar nan.

“ Gwamnati na kokarin samo mafita wadda za ta kasance dukkan fadin kasar nan an amince kuma an gamsu da ita.”

Da ga nan sai ya roki ‘yan Najeriya da kowa ya bayar da ta sa gudummawar domin ganin an kawo karshen wannan rikici.

Share.

game da Author