TARIN FUKA: Sai fa mun yi masa taron dangi wajen kau da shi a Najeriya ko kuma mu kwan ciki

0

Wasu kwararru a fannin kiwon lafiya sun yi kira ga gwamnati da ta maida hankali wajen kara ware kudade domin kawo karshen cutar tarin fuka a kasar nan.

Kwararrun sun yi wannan kira ne a taron tunatar da juna da aka yi a Abuja ranar Laraba.

Taron wanda akayi wa taken taken ‘Hada hannu da kungiyoyin bada tallafi domin kawar da cutar a Najeriya’ ya sami nasaran karkato da hankalin wakilan gwamnati, kungiyoyin bada tallafi na ciki da wajen kasa, kungiyoyin kare hakin dan adam, ma’aikatan kiwon lafiya wajen halarta taron.

Babban dalilin shirya wannan taro da kungiyar ‘Stop TB Partnership in Nigeria’ ta yi shine domin a hadu a tattauna hanyoyin da za su fi dacewa wajen dakile yaduwar cutar.

Babbar bakuwa a taron itace uwar gidan shugaban kasa Aisha Buhari kuma bayanin cewa lalle ya kamata hadu domin kawo karshen wannan cutar wanda a yanzu haka ya zama daya daga cikin cututtukan dake kisan mutane a duniya.

Aisha ta ce rashin iya gano cutar da wuri a jikin mutum da rashin ware isassun kudade domin kawar da cutar na cikin matsalolin dake hana a samun ci gaba a kawar da cutar.

Ta ce za ta yi amfani da matsayin da take da shi a kasar nan domin karkato da hankalin sassan gwamnati wajen yaki da kawar da cutar a kasan.

“ Ina kuma kira ga duk fannoninn kiwon lafiya dake kasar nan da a hada hannu da gwamnati wajen ganin an dakile yaduwar cutar.

Itama jami’ar kungiyar ‘Stop TB Partnership in Nigeria’ Lucica Ditiu ta ce kamata ya yi mutane su daina ganin tarin fuka a matsayin cutar da za a iya kawar da shi a asibiti kawai wai shikenan.

“ Dole kowa ya zo a hada hannu don hana yaduwar cutar wanda idan ba an yi masa taron dangi ba, an kawar dashi cutar zai halaka mutane da dama a kasar nan.”

Lucica ta ce a dalilin haka suke kira ga duka fannonin kiwon lafiya a kasar nan da a zo a surfafi wannan cuta don kawo karshen yaduwar da yake yi.

ABIN DA BINCIKE YA NUNA GAME DA CUTAR A NAJERIYA

Sakamakon bincike ya nuna cewa Najeriya n kasa ta shida a duniya da tarin fuka ya yi wa katutu. Sannan a Nahiyar Afrika kuwa Najeriya ce ta fi yawan mutanen dake dauke da cutar.

Sakamakon binciken ya nuna cewa masu dauke da tarin fuka a Najeriya sun kasu gida uku ne, Akwai mutanen dake dauke da cutar batare da sun sani ba, mutanen da suka kamu da cutar saboda kamuwa da suka yi da Kanjamau da wadanda ke dauke da cutar amma magani baya aiki gaba daya a jikin su.

Ya ce mafi yawan mutanen dake fama da wannan cuta na zaune ne a yankin karkara wato kauye.

Haka na da nassaba ne da matsalar rashin iya gano cutar da wuri a jikin mutane, rashin ware isassun kudade domin kawar da cutar, rashin kwararrun ma’aikata da rashin kayan aiki musamman a cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

A yanzu haka ana hasashen cewa mutane 407,000 ne ke kamuwa da cutar duk shekara domin a cikin adadin yawan mutanen dake dauke da cutar kashi 25 bisa 100 ne kadai ke samun kula.

Bayanai sun nuna cewa a kwani mutum daya dake dauke da cutar zai iya harban mutane 10 zuwa 15 da cutar a shekara idan baya shan magani.

Jami’in KUNGIYAR KIWON LAFIYA (WHO) Ayodele Awe yace tarin fuka cuta ce da ke warkewa a jikin mutum sannan ma za a iya hana yaduwarta idan gwamnati ta ware kudaden da ake bukata sannan an dage wajen wayar da kan mutane game da cutar da yadda za a kiyaye kamuwa da cutar.

Share.

game da Author