Shugabannin Kasashen Afrika 11 suka halarci bikin Ranar Dimokradiyya, babu na Najeriya ko daya

0

Akalla shugabannin kasashen Afrika 11 ne suka halarci bikin Ranar Dimokradiyya ta farko a 12 Ga Yuni a Najeriya, jiya Laraba.

Daga cikin su akwai Shugaban Chadi Idris Deby; Shugaban Mauritania, Mohammed Ould Abdel Aziz; Paul Kagame na Rwanda, George Weah na Liberiya, Dennis Sassou Nguesso na Congo da kuma Nana Akufo-Addo na Ghana.

Sauran sun hada da Emmerson Mnangawa na Zimbabwae; Macky Sall daga Senega; Adama Barrow daga Gambia da kuma Mahamadou Issoufou daga Jamhuriyar Nijar.

Shi ma Firayi Ministan Uganda, Ruhakana Rugunda shi ma ya samu halartar bikin da aka gudanar a Dandalin Eagle Square, Abuja.

Shigar sa filin taron ke da wuya sai Buhari ya rika bin wadannan shugabanni daya bayan daya ya na gaisawa da su. Tare kuma da gaisawa da sauran wakilan shugabannin kasashen duniya da suka halarata.

Buhari ya isa filin da karfe 10.5 inda ya kalli faretin sojoji da na ‘yan sanda, daga nan kuma aka kewaya da shi cikin filin a kan wata budaddiyar mota.

Sauran manyan baki sun hada da Mataimakin sa Yemi Osinbajo, matar sa Dolapo, Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan da kuma Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila.

An maida ranar 12 Ga Yuni ta zama ranar Dimokradiyya, tare da karrama marigayi MKO Abiola, wanda aka hakkake shi ne ya ci zabe, amma aka ki bayyana sakamako.

Abiola ya yi takara a karkashin rusasshiyar jam’iyyar SDP, inda ya kara da Bashir Tofa wanda ya fito wa rusasshiyar jam’iyyar NRC takara.

A cikin shekaru 19 baya, Najeriya na gudanar da bikin ranar dimokradiyya ce a ranar 29 Ga Mayu, wadda aka canja daga wannan shekara.

Daga yau 29 Ga Mayu za ta zama ranar rantsar da sabon shugaban kasa ko gwamnoni kawai.

Share.

game da Author