Tilas mu kori yunwa daga Najeriya –Tinubu

0

Jagoran jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya bayyana cewa kalubalen matsalolin tsaron da suka hada da ta’addanci, rikicin Fulani da makiyaya, hare-haren samame, garkuwa da mutane da fashi da makami sun kara ruruta wutar fatara da yunwa a kasar nan.

Tinubu wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Lagos, ya yi wannan bayani ne a cikinn wata takarda da ya fitar a ranar Tunawa da zagayowar dimokradiyya, wato 12 Ga Yuni.

“Tilas sai mun tashi tsaye mun kara yin hobbasa domin mu kori yunwa daga Najeriya. Wannan kuwa babban nauyi ne da ya wajabta tilas mu sauke shi.

Haka tsohon gwamnan na jihar Lagos tsakanin 1999 zuwa 2007 ya bayyana a cikin takardar da ya fitar ga manema labarai.
Ya nemi a goya wa Shugaba Muhammadu Buhari baya ganin yadda ya sadaukar da ranar 12 Ga Yuni ta zama Ranar Dimokradiyya a Nejeriya.

A kan haka ne Tinubu ya ce a hada hannu domin a karfafa ginin Najeriya ta hanyar korar fatara da yunwa a kasar nan.

Daga nan sai ya ce bai kamata a yi wa dimkoradiyyar da mu ke shan inuwar ta a yanzu rikon-sakainar-kashi ba, domin sai da aka sha rana aka sha gumi da wahala kafin a tabbatar da kafuwar ta.

Tinubu ya ce ya na goyon bayan yin amfani da tafarkin dimokradiyya wajen korar munanan matsalolin da suka addabi kasar nan, musamman ma fatara da yunwa, fashi da makami, ta’addanci da kuma garkuwa da mutane.

Da ya ke magana a kan ranar 12 Ga Yuni, Tinubu ya ce ranar 29 Ga Mayu ta na da muhimmanci, amma a tuna ita kawai ranar ce da ake tuna ranar da sojoji suka damka mulki a hannun farar hula.

A kan hana ne sai ya ce ranar 12 Ga Yuni ta fi ranar 29 Ga Mayu muhimmanci a kasar nan.

Share.

game da Author