Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yau Alhamis a zauren majalisa.
Idan ba a manta ba, Hukumar Zabe ta ki ba Okorocha Satifiket din zabe bisa zargin Tilasta wa malamin zabe da ya bayyana shi wanda yayi nasara da karfin tsiya.
Sai dai tun a wannan lokaci, Okorocha ya ce wannan zance ba daidai bane wadda a dalilin haka ya garzaya kotu.
Bayan sauraren karar, kotu ta yanke hukuncin da INEC ta tabbata ta mika wa Okorocha Satifiket din sa domin Malamin zabe ne kawai yake da ikon bayyana wanda yayi nasara da wanda baiyi ba. Kuma ya bayyana Okorocha a matsayin wanda yayi nasara a zaben Imo din.
INEC ta mika masa Satifiket din ranar Talata sai dai ta ce zata daukaka wannan kara da aka yanke wa wannan hukunci a kotu.