Sanata mai wakiltar Imo ta Yamma, Rochas Okorocha, ya ja kunnen ‘yan ‘uwan sa kabilar Igbo da su daina rudin kan su wajen su fa sai Igbo sun yi shugabancin Najeriya.
Okorocha ya yi wannan kakkausan gargadi ne a lokacin da aka rantsar da shi a ranar Alhamis. Ya ce masu rudin kan su da wannan ajanda su na neman ruwa ne kawai a cikin sahara.
Okorocha ya ce ba a neman shugabanci gaba-gadi, sai an bi matakan da suka dace.
Tsohon gwamna na jihar Imo, ya ce shi ya fi damuwa da Najeriya ta samu shugaba wanda zai kawo ingantaccen ci gaba da kara inganta rayuwar al’umma ko ma dan wace kabila ne.
“Shi mulki ai ba daukar shi ake haka kawai sororo a damka wani ba. sai an fito an nema. Bai yiwuwa Yankin Kudu Maso Gabas ya zauna ya rike hannaye, sannan ya rika mafarkin wai za a ba shi mulkin Najeriya.
“Sau da yawa ba a neman mulki da son kai ko nuna bangaranci. Ana batun abubuwan da ke bayyane a kasa ne.
“Ita dimokradiyya mulki ne na daukacin jama’a, don haka kabilar Igbo su kadai ba za su iya samar wa kan su shugaban kasa ba. Ban ga dalilin surutan da ake yi wai ‘a ba kabilar Igbo shugabancin kasa ba’. Maganar ma kwata-kwata ba ta a kan tsari. Wannan batu ya danganta da yadda ‘yan sauran shiyyoyin kasar na suka kale shi.
“Ni a nawa ra’ayin shi ne a bayar da mulki ga duk wanda aka san zai iya ciyar da kasa da al’umma gaba, ba tare da la’akari da kabilar sa ko addinin sa ba.”
Daga nan sai ya ce ya kamata yankin Kudu maso Gabas ya dinke barakar da ke tsakanin sa da sauran yankuna, idan har ya na so ya rika taka muhimmiyar rawa a siyasar kasar nan.
“Akwai bukatar Igbo su dinke barakar da ke tsakanin su da sauran yankunan kasar nan. Amma matsayin da mu ke a yanzu ba zai kai mu ga ci ba. mun kasance ba mu nan, kuma ba mu can. Mu ba a cikin jam’iyya mai mulki ba, mu kuma ba wata faffaka mu ke yi a cikin jam’iyyar adawa ba.”
Daga nan ya ci gaba da zayyana kudirorin da ya ke dauke da su a majalisar dattawa, ciki har da ganin an samar da ilmi kyauta.