Kwanturola Janar na Hukumar Kwastan ta Kasa, Hameed Ali, ya bayayyana cewa Hukumar Kwastan ta na tara akalla naira bilyan 5.5 a kowace rana.
Ali ya furta haka jiya Alhamis a lokacin da ya kai ziyara a hedikwatar kungiyar dillalan fiton kayan da ake shigowa da su ta ruwa (NAGAFF), a ofishin na su da ke Lagos.
Ali ya kara da cewa an samu wannan karin kudaden shiga ne sakamakon maida tsarin tattara kudaden shiga da aka yi zuwa na zamani a kowace tashar jiragen ruwan kasar nan.
Ya ce wannan karin samun kudaden shiga ya sa hukumar kwastan na biyan albashin ma’aikatan ta a kan lokaci, kuma tsarin ya kara maida hukumar daya daga cikin muhimman hukumomin da gwamnatin tarayya ke takama da ita wajen samar da kudaden shiga.
“Wannan tsari ya haifar da hanyoyin shigar kudade aljihun gwamnati kai tsaye kuma a cikin sauki a tashoshin jiragen ruwa da kuma kan iyakokin kasar nan.
“Ya kuma magance duk wata hanyar da kudade za su rika sulalewa, kasancewa kai tsaye ake biyar kudade, ba tare da an yi cudanya tsakanin mai biyan kudi da mai karbar wa gwamnatin kudaden ba.
Daga nan ya ja kunnen ‘yan kungiyar da su rika gudanar da ayyukan su a bisa ka’dojin da gwamnati ta gindiya, ba tare da kumbiya-kumbiya ba.
Shugaban NAGAFF, kuma wanda ya kafa kungiyar, Boniface Aniebona, ya roki dukkan masu amfani da tashoshin jiragen ruwa su taimaki gwamnati ta hanyar bi da kuma kiyayewa da ka’idojin da aka shimfida musu.
Discussion about this post