• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    court

    Mijina malalaci kuma rago ne, na gaji – Korafin Latifat a Kotu

    ‘Yan sanda sun damke faston da ake zargin yayi wa ‘yar shekara 19 fyade

    ‘Yan sanda sun kama wani da ya shahara wajen yi wa mutane damfara ta Facebook

    #EndSARS: Majalisar Dinkin Duniya ta yi magana kan zargin kisan masu zanga-zanga a Lekki, Lagos

    Za a shiga mummunar yanayi a Gaza idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba – MDD

    Abuja bill-board

    RASHIN TSARO – Abuja ta zama matattarar batagari da masu sace mutane – Dan majalisa

    NYSC

    Za a yi wa shirin yi wa kasa hidima, NYSC, garambawul – Gwamnati

    Gwamnatin Tinubu ba za ta ƙaƙaba wa jama’a takunkumin hana magana ba – Minista

    SHIRIN WAYAR DA KAI: Ministan Yaɗa Labarai ya kafa kwamitin tsara daftarin cusa ɗa’a, kishin ƙasa da kyawawan ɗabi’u

    KISAN MASU MAULIDI: Mun samu gawarwaki 85 – Hukumar Agajin Gaggawa

    KISAN MASU MAULIDI 85: Sarkin Musulmi, Shehunan Tijjaniya, Dattawan Arewa da Shugaban Izala sun ce ba za a yafe ba

    TARON COP28: Su Tinubu da sauran tawagar Najeriya ba sharholiya ce ta kai su Dubai ba – Minista Idris

    TARON COP28: Su Tinubu da sauran tawagar Najeriya ba sharholiya ce ta kai su Dubai ba – Minista Idris

    Uba Sani ya yi alhini da ta’aziyyar kisan dandazon ƴan maulidi a Kaduna, ya umarci a gudanar da bincike

    Uba Sani ya yi alhini da ta’aziyyar kisan dandazon ƴan maulidi a Kaduna, ya umarci a gudanar da bincike

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Saura ƙiris Liverpool ta zubda abin faɗi a wasan Premier League na ranar Lahadi

    Saura ƙiris Liverpool ta zubda abin faɗi a wasan Premier League na ranar Lahadi

    MESSIN DAI: Leo Messi ya lashe kyautar ɗan kwallon duniya ta Ballon d’Or a karo na takwas

    MESSIN DAI: Leo Messi ya lashe kyautar ɗan kwallon duniya ta Ballon d’Or a karo na takwas

    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Dalilin da ya sa na ziyarci Tinubu – Uba Sani

    BIDIYO: Dalilin da ya sa na ziyarci Tinubu – Uba Sani

    BIDIYO: Tinubu masoyin ‘Yan jarida ne – Idris

    BIDIYO: Tinubu masoyin ‘Yan jarida ne – Idris

    Timipre-Sylva

    TANGARƊA A APC: Kotu ta hana Sylva, tsohon Ministan Fetur tsayawa takarar zaɓen gwamnan Bayelsa

    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

No Result
View All Result

Lallai Ku Fahimci Gwamna Ganduje Baya So Ayi Sulhu, Daga Imam Murtadha Gusau

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
June 14, 2019
in Ra'ayi
0
Ganduje Umar

Ganduje Umar

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Assalamu Alaikum

Ya ku bayin Allah! Kamar yadda kuka sani, yin sulhu tsakanin mutane guda biyu da basa jituwa, ko suka samu sabani, ko kuma sulhunta mutane biyu da basa ga maciji da juna ko basa jituwa, ko suka samu rashin fahimta, abu ne da shari’ar Musulunci ta kwadaitar, ta karfafa, kuma ta kira Musulmi da suyi kokarin yi, musamman a duk lokacin da suka samu sabani tsakanin su.

Kuma dukkanin mu mun san cewa, yana daga cikin kyawawan dabi’u na kwarai, sulhunta mutane. Kuma abu ne da aka kira al’ummar Musulmi da su yawaita yi tsakanin su domin samun zaman lafiya, kamar yadda Allah madaukakin Sarki yace:

“Kuma kuji tsoron Allah kuyi sulhu tsakanin ku.” [Qur’an 8:1]

Imam Murtada Gusau
Imam Murtada Gusau

Sannan sulhunta mutane daya ne daga cikin ayukkan da suke jawo wa mutane lada mai yawa, kuma yake samar da rahamar Allah tsakanin su. Saboda yin sulhu tsakanin mutane yana kawar da kiyayya tsakanin mutane, sannan zukatansu su tsarkaka. Allah ta’ala yace:

“Babu alkhairi a cikin mafi yawan ganawar su, sai dai fa wadanda suka yi umurni da yin sadaka ko umurni da kyakkyawan aiki, ko kuma yin sulhu tsakanin mutane. Duk wanda ya aikata wannan yana mai neman yardar Allah to zamu saka masa da sakamako mai girma.” [Qur’an 4:114]

Saboda haka a wannan aya ta Alkur’ani mai girma mun fahimci cewa sulhunta mutane al’amari ne mai muhimmanci matuka, da ya zama wajibi Musulmi suyi riko da shi a rayuwar su domin samun tsira duniya da lahira. Domin a cikin yin sulhu ne zukata suke zama daya, kuma a cikin yin sulhu ne ake samun hadin kai, zaman lafiya da cigaba. Kuma wallahi rashin yin sulhu da yin watsi da muhimmancin sa, zai iya zama sanadiyyar rugujewa da rushewar al’ummar Musulmi gaba daya! Allah ya kiyaye, amin. Shi yasa addinin Musulunci ya sanya yin sulhu tsakanin mutane sama da komai, kuma sama da mafi yawancin Ibadu. Annabi (SAW) yace:

“Shin ba zan shaida maku abinda yafi Sallah, Azumi da Sadaqah ba? Sai Sahabbai suka ce eh, ya Manzon Allah. Sai Annabi (SAW) yace: “yin sulhu tsakanin mutane, domin kiyayya da husuma masu aske wa ne (wato rusa Imanin bayin Allah).” [Ahmad, Abu Dawud da Tirmizi ne suka ruwaityo]

Kuma Annabi (SAW) yace:

“Baya halatta Musulmi ya kauracewa dan uwansa Musulmi sama da kwanaki uku. A duk lokacin da suka hadu suna juyawa juna baya. Mafi alkhairi a cikin su shine wanda ya farawa da juna sallama.” [Ahmad]

Kuma Imam Al-Awza’i Allah ya jikan sa da rahama yace:

“Babu wata tafiya ko wani taku da Allah yafi so fiye da yin tafiya domin yin sulhu tsakanin mutane. Duk wanda ya sulhunta mutum biyu Allah ta’ala za ya bashi kariya daga azabar wuta.”

Sannan Annabi (SAW) yace:

“Ana bude kofofin rahama na Aljannah a duk kwana biyu: Ranar Litinin da Alhamis. Duk wani bawa da bai taba yin shirka da Allah ba, za’a gafarta masa, sai dai fa banda wadanda suke fada tsakanin su da juna, kuma suke gaba da juna. Za’a umurci Mala’ika cewa, kar ka raba rahamar Allah da su, har sai sunyi sulhu tsakanin su.” [Muslim]

Ya ku ‘yan uwa na masu girma, yin sulhu tsakanin mutane lallai al’amari ne mai girman gaske. Jama’ah mu kalli girman munin karya da hadarin ta, amma duk da haka akace ya halatta Musulmi yayi karya domin ya sulhunta mutane biyu da basa jituwa, ko jama’ar da suke fada da junansu!

Ya ku jama’ah! Kamar yadda kuka sani, a bisa kiraye-kiraye da jama’a suka yi tayi a kafafen yada labarai kamar radio, talabijin, jaridu da kuma kafafen yada labarai na zamani da ake kira soshiyal midiya, na ganin cewa manya sun shiga cikin rikicin da ke gudana tsakanin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, domin cigaban Kano, arewacin Najeriya da ma Najeriyar baki daya.

Alhamdulillah, kamar yadda kuka sani, wannan kiraye-kiraye sunyi tasiri matuka, domin fadar mai girma shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, sun sanya baki domin sulhunta wadannan shugabanni, domin samun zaman lafiya mai dorewa da ci gaba.

An fara zama a babban birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja, domin tattauna batun wannan sulhu, kuma a bisa sahhale wa da kuma sa idon fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari. Wanda daga karshe aka kafa wani kwamiti da ke dauke da wasu gwamnonin jihohi masu mutunci, da kuma wasu mutane masu daraja da mutunci, da za ya cigaba da tattaunawa har Allah yasa ayi cikakken sulhun da ake bukata.

Ya ku jama’ah! Kamar yadda kuka sani, duk mun san me ake kira sulhu. Domin sulhu shine, idan wani daga cikin wadanda ake so a sulhunta yayi abunda yake ba daidai ba sai a fada masa gaskiya, kuma ya jaye wannan abun da yayi, a koma yadda ake ada can, a yafi juna. Misali, duk wanda yasan tarihin masarautun kasar Kano, yasan cewa Sarki daya aka sani. Don haka kenan idan dai har sulhu ake son yi da gaske, to a koma yadda ake da can farko. Wadancan “Sarakuna” da Gwamna Ganduje ya kirkiro, a bisa wata doka tasa ta kashin kansa da ya kirkira, cikin wani dan kankanin lokaci, mara tushe bare makama, su koma hakimansu da suke a can farko!

Amma duk da wannan yunkuri da mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari yake yi na ganin cewa anyi sulhu, domin samun zaman lafiya, sai kwatsam muka ji wai Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya gindaya wasu sharudda ga Mai Martaba Sarki Sanusi wanda yace wai sune, matakin tabbatar sulhu tsakaninsa da Sarkin na Kano.

Wanda kamar yadda labari ya riske mu, wai Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a wata takarda mai dauke da sa hannun Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kano Kwamared Muhammad Garba. Daga cikin sharuddan da Gwamna Gandujen ya gindaya wa Mai Martaba Sarkin, akwai batun cewa wai sai Sarkin Kanon ya fito fili ya nemi afuwar Gwamnan tare da al’ummar Jihar Kano game da wulakanta darajar Masarautar Kano da yayi ta hanyar tsoma baki a cikin harkar siyasa!

Sannan wai kuma sai an janye kararrakin da aka shigar kotu, sanadiyyar kirkirar wadancan masarautu marasa asali da Gwamnan yayi.

Har ila yau wai kuma Gwamna Ganduje ya bayyana cewa, akwai bukatar Sarkin yayi mu’amala ta aiki da sabbin Sarakunan masarautun da aka kirkira guda hudu a matsayinsa na Shugaban Sarakunan, kuma gogagge, kwararre, masanin tattalin arziki, domin su bada gudummawa wajen ciyar da jihar Kano gaba.

Ya kai mai girma shugaban kasa, Malam Muhammadu Buhari! Ya ku jama’ar Najeriya! Ku sani, a bisa wadannan sharudda da Gwamna Ganduje ya gindaya, ya kamata ku fahimci cewa lallai Gwamnan baya son ayi sulhu, kuma baya nufin a samar da zaman lafiya, kuma baya nufin Kano, arewa da Najeriya da alkhairi. Domin idan ba haka ba, me yake nufi da wadannan sharudda? Sharuddan da yana sane, sun saba doka, kuma basa kan hanya, kuma basa bisa ka’idah? Sharuddan da yasan cewa Sarki Sanusi da duk wani mai son gaskiya da kaunar zaman lafiya ba zai yarda da su ba sam!

Haba jama’ah! Wane irin al’amari ne wannan? Shidai wannan bawan Allah, wato Mai Martaba Sarki, har kullun sai kunyi kokarin kirkiro abun da zai cutar da shi kuma ya cutar da wannan masarauta mai daraja, mai dimbin tarihi? Saboda haka, ya mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari, muna rokon ka, don Allah, don Allah, don Allah ka taimaka domin ganin anyi wa wannan bawan Allah adalci, kuma anyi wa wannan masarauta ta Kano adalci! Domin a gaskiya, mu mun cire rai na cewa, Gwamna Ganduje ba zai iya yiwa Sarki da masarautar Kano adalci ba!

Saboda haka, wadannan sharudda da Gwamna ya gindaya kawai mafarkin sa ne, tunanin sa ne, kuma sam ba zai yiwu ba. Domin bamu yarda Mai Martaba Sarki yayi laifin da Gwamna yake cewa wai ya nemi afuwa ba. Sannan Sarakunan da yake cewa Mai Martaba yayi aiki tare da su, kowa yasan cewa basu bisa doka, kuma basu bisa ka’idah. Sannan bayan haka, Gwamna ya sani, magana tana kotu, kuma ba Mai Martaba ne ya shigar da kararraki ba bare yace ya janye kararrakin. Sannan kuma Alhamdulillahi, a wannan mulki na mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari kotuna a Najeriya suna aiki bisa adalci, kuma da yardar Allah muna da yakinin za’ayi muna adalci.

Saboda haka duniya ta sani, wadannan sharudda na Gwamna Ganduje shirme ne, kuma basu da tushe bare makama, kuma sam wallahi bamu yarda da su ba!

Watakila zamu iya amincewa Mai Martaba Sarki ya bada hakuri, idan har ma yayi laifin, amma da sharadin idan kaima ka tabbatarwa da duniya cewa faifan Video na Dollars da aka kama ka kana zubawa aljihu gaskiya ne.

Sannan da sharadin cewa ka tabbatarwa da duniya kudi da aka ce Gwaggon Biri ya cinye a gidan Zoo na Kano karya ne.

Sannan ka tabbatarwa da duniya cewa zaben ka da aka yi karo na biyu, mai cike da zalunci, rudani, shirme da karya, haramtaccen zabe ne, bana halal ba.

Sannan ka tabbatarwa da duniya cewa ginin Masallacin Idi da ake yi ba daidai bane, son zuciya ne tsantsa.

Ya kai Gwamna, lallai idan kayi haka, to tabbas zamu amince Mai Martaba Sarki ya baka hakuri bisa abunda kake gani kai a wurin ka laifi ne, amma mu mun san cewa naka laifin shine mafi munin laifi. Domin dumu-dumu aka kama ka kana karbar cin hanci da rashawa, wanda Annabi Muhammad (SAW) ya fada karara cewa Allah ya tsine wa mai bayar wa da mai karbar sa!

Kaga kai kana cikin ruwa dumu-dumu tsakanin ka da mahaliccin ka. Domin maganar Annabi Muhammad (SAW) Wallahi ba zata tashi a banza Ba.

Idan kuma har kai Gwamna Ganduje baka bada hakuri ga Jama’ar Jihar Kano ba akan laifin da kayi masu, to ta yaya kake tsammanin Mai Martaba Sarki ya bada hakuri akan laifin da sam bai yi ba? Kirkira kawai aka yi aka dora masa, domin aci mutuncin sa da mutuncin masarautar Kano?

Daga karshe, ina rokon Allah ya taimaki Mai Martaba Sarki. Allah ya karya Makiyan sa. Allah ya cigaba da karya dukkan wata nasarar magautan Sarki a duk inda suke. Jihar Kano, Arewa da Najeriya baki daya, Ya Allah ka cigaba da wanzar da zaman lafiya tare da yalwar arziki a cikin su. Amin.

Wassalamu Alaikum,

Dan uwan ku: Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.

Tags: AbujaGandujeHausaKanoNajeriyaPREMIUM TIMES
Previous Post

Masu rajin a ba kabilar Igbo shugabancin Najeriya tatsuniya su ke yi – Okorocha

Next Post

A daina kira na ‘Matan Buhari’, akira ni First Lady’, Uwargidan shugaban kasa – Inji Aisha Buhari

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
A daina kira na ‘Matan Buhari’, akira ni First Lady’, Uwargidan shugaban kasa – Inji Aisha Buhari

A daina kira na 'Matan Buhari', akira ni First Lady', Uwargidan shugaban kasa - Inji Aisha Buhari

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Yadda farashin magungunan Mura, Zazzabi, da sauransu suka yi tashin gwauron zabi cikin shekaru Hudu a Najeriya
  • DUBU TA CIKA: ‘Yan sandan Adamawa sun cafke wani matashi da ya rika yi wa babbar Zakara fyade yana lalata da wannan Zakara
  • Gwamnati ta fara horas da ma’aikatan lafiya hanyoyin dakile yaduwar cutar diphtheria
  • Mijina malalaci kuma rago ne, na gaji – Korafin Latifat a Kotu
  • KISAN TUDUN BIRI: Uba Sani ya zama Uba da Uwa ga ya’yan da suka rasa iyaye a sanadiyyar harin

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.

No Result
View All Result
  • Labarai
  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.